Wata Sabuwa: Babban Abin da Amurka da Iran Ke Rigima a Kai yayin Tattunawa

Wata Sabuwa: Babban Abin da Amurka da Iran Ke Rigima a Kai yayin Tattunawa

  • Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta ci gaba da tattaunawa a birnin Islamabad na kasar Pakistan kan yakin Gabas ta Tsakiya
  • Tawagar kasashen biyu sun gana gaba da gaba yayin da ake yunkurin cimma yarjejeniyar da za ta kawo karshen yakin
  • A yayin tattaunawar ta wakilan na kasashen biyu, an samu wani bangare wanda suka samu sabani a tsakani a kansa

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Islamabad, Pakistan - Tawagar kasashen Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran na tattaunawa a birnin Islamabad na kasar Pakistan.

Kasashen biyu na tattaunawa ne domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da nufin kawo karshen yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Iran da Amurka na tattaunawar zaman lafiya a Pakistan
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da takwaransa na Amurka, Donald Trump Hoto: @drpezeshkian, @RealDonaldTrump
Source: Twitter

Amurka da Iran na tattaunawa

Tashar Tasnim da ke da alaƙa da Gwamnatin Iran, ta tabbatar da cewa ƙasar Iran da Amurka suna musayar saƙonni a rubuce bayan tattaunawa.

Kara karanta wannan

An kammala tattaunawa ta farko, an ji yadda ta kaya tsakanin Amurka da Iran

Ta bayyana cewa ana musayar sakonnin ne domin ƙoƙarin cimma matsaya guda kan tsarin da tattaunawar za ta bi.

Yayin da take ambato wakilinta da ke babban birnin Pakistan, ta ce an samu cikas wajen samun ci gaba sakamakon abin da ya kira “bukatun wuce gona da iri” daga ɓangaren Washington.

Kasar Amurka na gabatar da bukatu

Ta kuma bayyana cewa har yanzu ana tsaka da tattaunawa, sai dai batun mashigar Hormuz na ɗaya daga cikin mahimman abubuwan da ake da babban saɓani a kai.

Wakilin ya bayyana cewa:

“Bayan tattaunawar fuska-da-fuska tsakanin masana daga tawagogin Iran da Amurka a Islamabad, ɓangarorin biyu sun ci gaba zuwa matakin musayar rubutaccen bayani domin cimma matsaya ɗaya kan tsarin tattaunawar."
"Sai dai tawagar Amurka ta kawo cikas ga ci gaban tsarin ta hanyar buƙatunta na wuce gona da iri."
Har yanzu ana ci gaba da tuntuɓar juna, amma Iran tana nan a kan matsayinta na kare nasarorin da ta samu ta fuskar soja, sannan tana jaddada cewa dole ne a tabbatar da haƙƙoƙin al’ummar Iran.

Kara karanta wannan

Sabon shirin yaki: Amurka ta fadi manyan makaman da ta zargi China za ta ba Iran

Wane abu ake takaddama a kai?

Batu na mashigar Hormuz ya kasance babban ƙalubale inda ake samun rashin jituwa mai tsanani, tashar Aljazeera ta kawo rahoton.

Tun da fari, wata majiya ta kusa da tawagar tattaunawar ta Iran ta bayyana cewa akwai yiwuwar a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawar tsakanin Iran da Amurka a daren yau ko kuma gobe.

Iran da Amurka na tattaunawa a Pakistan
Tawagar Iran yayin da ta sauka a Pakistan don tattaunawa da Amurka Hoto: @Visegrad
Source: Twitter

Wakilin na Tasnim ya bayyana a daren Asabar ɗin nan cewa an kammala wani mataki na tattaunawar fuska-da-fuska, inda ya lura cewa a halin yanzu tawagogin biyu suna kan matakin musayar saƙonni ne a rubuce.

Hakan na nuna cewa duk da an fara tattaunawa, har yanzu akwai sabani a kan buƙatun ɓangarorin biyu, musamman kan ikon zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

Iran ta karyata Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta yi martani kan batun cewa jiragen ruwan Amurka sun ratsa mashigar ruwan Hormuz.

Iran ta fitar da sanarwa inda ta karyata rahotannin da ke cewa jiragen ruwan sun ratsa mashigar Hormuz.

Wani babban jami’in soja yana cewa babu wani jirgin Amurka da ya ketare mashigar, yana mai ƙaryata rahotannin da aka fara yadawa kan batun.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng