"Ban da Wuce Gona da Iri": Iran Ta Gargadi Amurka kan Kutse Ta Mashigar Hormuz

"Ban da Wuce Gona da Iri": Iran Ta Gargadi Amurka kan Kutse Ta Mashigar Hormuz

  • Daular Musulunci ta Iran ta musanta rahoton cewa jiragen ruwan Amurka sun ratsa ta mashigar Hormuz da ta datse
  • Duk da ana tattaunawa kan yin sulhu a Pakistan, Iran ta yi barazanar kai hari cikin mintuna 30 idan jirgin Amurka ya so ketare yankin
  • Yaƙin Iran ya jawo tangarda ga kasuwancin mai da iskar gas a duniya wanda yawancin jiragen da ke ɗakin man ke ratsa wa ta mashigar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Ƙasar Iran – Wani babban jami’in sojan Iran ya karyata rahotannin da ke cewa wani jirgin ruwan Amurka ya ratsa mashigar Hormuz yayin da ake ƙoƙarin sulhu.

Wannan martani ya zo ne bayan wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka sun fara bada rahoton cewa jiragen ruwan rundunar sojin ruwan Amurka sun bi ta wannan muhimmiyar mashiga.

Kara karanta wannan

Iran ta gano karyar da Amurka ta sharara kan mashigar Hormuz, ta fadi gaskiya

Iran ta ja kunnen Amurka
Mojtaba Khamenei da Donald Trump na Amurka Hoto: Imam Sayyid Mojtaba Khamenei/Donald J Trump
Source: Facebook

New York Post ta wallafa Iran ta kuma yi gargaɗi mai tsauri ga duk wani jirgin sojan Amurka, inda ta ce za ta kai hari cikin mintuna 30 idan aka kuskura aka ketare mashigar Hormuz.

Iran ta gargadi Amurka

Daily Sabah ta wallafa cewa wannan gargadi ya nuna yadda tashin hankalin ke ƙaruwa tsakanin ɓangarorin biyu duk da ana batun na sulhu a Islamabad da ke Pakistan.

Sai dai wani rahoto daga wani jami’in Amurka ya tabbatar da cewa wasu jiragen ruwan ƙasar sun ratsa mashigar Hormuz a karon farko tun bayan fara yaƙin a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.

Rahotannin sun zo ne a daidai lokacin da ƙasar Pakistan ke jagorantar tattaunawar neman kawo ƙarshen rikicin makamai a yankin Gabas ta Tsakiya.

Wannan rikici ya samo asali ne daga harin haɗin gwiwa na Amurka da Isra’ila kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026 wanda ya lashe jagoran addini na ƙasar, Ayatoullah Khamenei.

Kara karanta wannan

Trump ya fadi babbar barazana 1 da har yanzu Iran take da shi ga kasashen duniya

Pakistan ta shiga tsakanin Amurka da Iran

A baya-bayan nan, Pakistan ta taimaka wajen samar da tsagaita wuta na makonni biyu tsakanin Amurka da Iran, a wani yunkuri na rage zafin rikicin da ke barazana ga zaman lafiya a yankin.

Yaƙin ya janyo cikas mai tsanani ga zirga-zirgar mai da iskar gas ta LNG ta mashigar Hormuz, wacce ke da matuƙar muhimmanci ga kasuwancin makamashi a duniya.

Iran na iya kai wa duk jirgin Amurka da ketara Hormuz hari
Shugaban kasar Amurka Donald J Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

Wannan ya haifar da girgizar farashin makamashi a sassa daban-daban na duniya, yayin da farashi ya rika tashin gwauron zabo.

Dangane da asarar rayuka, hukumomin lafiya na Iran sun ce kusan mutane 3,000 ne suka mutu sakamakon yaƙin. A bangaren Amurka kuma, an tabbatar da mutuwar aƙalla sojoji 13, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Rikicin na ci gaba da jefa fargaba a duniya, yayin da ƙoƙarin sulhu ke fuskantar ƙalubale duk da matakan da ake ɗauka.

Yakin Iran: An kammala ganawar farko

A baya, mun wallafa cewa rahotanni daga majiyoyin da ke kusa da masu shiga tsakani sun tabbatar cewa an kammala matakin farko na tattaunawar kai tsaye tsakanin Amurka da Iran a Pakistan.

Kara karanta wannan

Amurka ta saki kadarorin Iran da ta rike kafin fara tattaunawa? Magana ta fito

Majiyoyin sun ce a yanzu bangarorin biyu na musayar takardu a rubuce domin tabbatar da cewa sun fahimci juna kan yarjejeniyoyin da aka cimma a yau Asabar 11 ga watan Afrilu, 2026.

Bayanan da ke ffitowa daga birnin Islamabad sun nuna cewa an yi zagaye da dama na tattaunawa cikin yanayi mai kyau, inda wakilan Amurka da Iran suka tattauna cikin fahimta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng