Ta Faru Ta Kare, An Fara Tattaunawa tsakanin Amurka da Kasar Musulunci ta Iran

Ta Faru Ta Kare, An Fara Tattaunawa tsakanin Amurka da Kasar Musulunci ta Iran

  • Tawagar Amurka karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, JD Vance ta fara tattaunawa da wakilan Iran a kasar Pakistan
  • Wannan zaman tattaunawa na zuwa ne kwanaki uku bayan tsagaita wuta a yakin da ya barke tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila
  • Rahotanni sun nuna cewa wakilan Amurka da na Iran sun gana da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif kafin shiga zauren tattaunawar da aka shirya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Islamabad, Pakistan - Rahotanni daga birnin Islamabad da ke Pakistan sun nuna cewa an shiga zauren tattaunawa tsakanin kasar Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Hakan na zuwa ne kwanaki akalla uku bayan tsagaita wuta a yakin da ya barke tsakanin Amurka, wacce ta yi hadin guiwa da kasar Isra'ila da kasar Iran.

Islamabad.
Wurin da aka shirya tattaunawar Amurka da Iran a birnin Islamabad na kasar Pakistan Hoto: Pool
Source: Getty Images

Amurka da Iran sun fara tattaunawa

BBC Hausa ta tabbatar a wani rahoto da ta wallafa yau Asabar, 11 ga watan Afrilu, 2026 cewa wakilan Amurka da na Iran sun fara tattaunawar sulhu a tsakaninsu a birnin Islamabad.

Kara karanta wannan

Iran ta faɗi babban matsalar Amurka a shirin yarjejeniyar zaman lafiya

Tun farko dai an samu rahoton cewa tawagar kasar Amurka karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, JD Vance ta isa birnin Islamabad domin fara wannan taro.

Bayan isa birnin da aka shirya wannan zama, Vance ya jagoranci tawagar Amurka sun gana da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif.

Wakilan Amurka da Iran sun gana da Sharif

Sauran mambobin tawagar Amurka da mataimakin shugaban ke jagoranta sun hada da wakili na musamman, Steve Witkoff da Jared Kushner, wanda ya kasance surukin Shugaba Donald Trump.

Haka zalika, wakilan kasar Musulunci ta Iran sun isa birnin Islamabad karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Iran, Abbas Aragchi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Firaministan Pakistan ya gana da tawagar Iran karkashin Abbas Araghchi kafin daga bisani ya tattauna da tawagar Amurka.

Shehbaz Sharif ya bayyana fatansa game da tattaunawar, wadda ya ce za ta zama matakin farko na samun zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Fadar White House ta yi magana

Bayan wannan ganawa da Sharif ne, tawagar Amurka ta shiga ganawa da wakilan kasar Iran domin tattaunawa kan yadda za a samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Babbar tawagar Iran ta isa Pakistan don tattaunawa da Amurka, an hada manyan mutane

Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa Fadar White House ta tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasa, JD Vance da tawagarsa sun fara tattaunawa gaba da gaba da wakilan Iran a Islamabad.

Dakin taro.
Yadda aka fara tattaunawa tsakanin wakilan Amurka da na Iran a Pakistan Hoto: Pool
Source: Getty Images

Ana sa ran wannan zama zai kawo karshen yakin Amurka/Isra'ila da kasar Iran, wanda aka tsagaita wuta na tsawon makonni biyu bayan shafe fite da wata guda ana musayar wuta.

An yi hasashen yadda za a cimma matsaya

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa na farko na Iran, Mohammad Reza Aref ya bayyana abin da zai kawo matsala a tattaunawar kasarsa da Amurka.

Aref ya bayyana cewa sakamakon tattaunawar da ke gudana a Islamabad zai dogara kacokan kan abubuwan da Amurka ta fi ba fifikon Amurka.

Aref ya ce akwai yiwuwar cimma yarjejeniya mai anfani ga kowa idan wakilan Amurka suka mayar da hankali kan muradunsu na “America First," sun kyale batun Isra'ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262