Amurka Ta Saki Kadarorin Iran da Ta Rike kafin Fara Tattaunawa? Magana Ta Fito
- Wani rahoto da aka fitar ya yi ikirarin cewa Amurka ta amince da sakin kadarorin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ta rike
- Rahotan ya nuna cewa Amurka ta amince ta saki kadarorin ne wadanda aka rike a kasar Qatar da wasu bankunan kasashen waje
- Wani babban jami'in Amurka, ya fito ya yi martani kan batun cewa Washington ta amince da sakin kadarorin kafin fara tattaunawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Wani babban jami’in Amurka ya yi magana kan batun cewa Washington ta amincr ta saki kadarorin Iran da aka rike.
Jami'in na Amurka ya ƙaryata rahoton da ke cewa Washington ta amince ta saki kadarorin Iran da aka rike a ƙasar Qatar da sauran bankunan ƙasashen waje.

Source: Facebook
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton maganar da jami'in ya yi a ranar Asabar, 11 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan
Iran ta dauki wani mataki da ya sa ta shiga gaban Amurka a shirin zaman sulhu a Pakistan
Kasar Iran da Amurka za su tattauna
Tawagar Iran da Amurka sun riga sun isa birnin Islamabad na ƙasar Pakistan domin tattaunawar da ke da nufin kawo ƙarshen yaƙi a Gabas Ta Tsakiya.
Tun da fari, Tehran ta bayyana cewa duk wata yarjejeniyar dindindin ta tsagaita buɗe wuta dole ne ta haɗa da sakin kadarorinta da aka sanya wa takunkumi, da kuma dakatar da yaƙin da Isra’ila ke yi da ƙungiyar Hezbollah a Lebanon.
Iran ta ce Amurka ta amince da bukatarta
Wata majiya daga Iran da ba a bayyana sunanta ba ta shaidawa tashar Reuters cewa Amurka ta amince ta saki kadarorin, kuma wannan matakin yana da alaƙa kai tsaye da tabbatar da tsaro a mashigar Hormuz.
Majiyar, wadda ta buƙaci a sakaya sunanta saboda nauyin maganar, ta ce sakin kadarorin "yana da alaƙa kai tsaye da tabbatar da zirga-zirga cikin aminci ta Mashigar Hormuz," wanda ake sa ran zai zama babban jigo a tattaunawar.
Majiyar ba ta faɗi adadin kuɗaɗen da Amurka ta amince za ta saki ba. Sai dai wata majiyar ta daban daga Iran ta ce Amurka ta amince ta saki dala biliyan 6 na kuɗaɗen Iran da ke ajiye a Qatar.
Majiyar ta farko ta yi maraba da wannan mataki (da Amurka ta ƙaryata) a matsayin alamar "gaske" wajen cimma yarjejeniya a tattaunawar Islamabad.
Ta ƙara da cewa wannan na ɗaya daga cikin buƙatun Iran a "saƙonnin da aka aika wa ɓangaren Amurka," kuma Tehran ta samu amincewar Amurka ta sakin kuɗaɗen.

Source: Twitter
Wane martani Amurka ta yi?
A cikin wani saƙo daga Fadar White House, wani babban jami’in Amurka ya mayar da martani ga rahoton inda ya ce:
“Ƙarya ne. Ba ma a fara tarurrukan ba tukunna.”
A ranar Asabar ɗin, ofishin Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya bayyana cewa ya gana da Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, a Islamabad, yana mai ƙara da cewa an fara tattaunawar zaman lafiya don kawo ƙarshen yaƙin Gabas Ta Tsakiya.
Jagoran addini na Iran ya samu raunuka
A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya samu raunuka a hare-haren Amurka da Isra'ila.
Majiyoyi sun bayyana cewa Mojtaba Khamenei ya samu raunuka a fuskarsa da kafafunsa amma yana murmurewa.
Hakazalika, sun bayyana cewa Mojtaba Khamenei yana sane da abubuwan da ke gudana a gwamnatin kasar Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

