Babbar Tawagar Iran Ta Isa Pakistan don Tattaunawa da Amurka, an Hada Manyan Mutane

Babbar Tawagar Iran Ta Isa Pakistan don Tattaunawa da Amurka, an Hada Manyan Mutane

  • Shirye-shirye sun kankama domin fara tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a birnin Islamabad na kasar Pakistan
  • Tawagar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta tura ta isa birnin Islamabad domin tattaunawa da Amurka kan yakin da ake yi
  • Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf ne yake jagorantar tawagar da aka tura

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Islamabad, Pakistan - Manyan jami’an gwamnatin ƙasar Iran sun isa birnin Islamabad na Pakistan, domin tattaunawar tsagaita wuta da Amurka.

Jami'an na Iran sun isa Pakistan ne a daidai lokacin da tashe-tashen hankula ke ci gaba da faruwa a yankin Gabas Ta Tsakiya.

Tawagar kasar Iran ta isa Pakistan
Jagororin tawagar Iran yayin da suka isa Pakistan Hoto: @Visegrad
Source: Twitter

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton isar jami'an gwamnatin Iran a Pakistan a ranar Asabar, 11 ga watan Afirilun 2026.

Tawagar Iran ta isa Pakistan

Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, da Ministan harkokin waje Abbas Araghchi ne ke jagorantar ɓangaren Iran a tattaunawar.

Kara karanta wannan

Iran ta dauki wani mataki da ya sa ta shiga gaban Amurka a shirin zaman sulhu a Pakistan

A ɓangaren Washington kuwa, mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ne ke wakiltar ƙasar, tare da wakili na musamman Steve Witkoff da kuma Jared Kushner.

Gabanin fara tattaunawar, Vance ya bayyana cewa Washington a shirye take ta yi tattaunawa ta gaskiya idan har Iran za ta yi tattaunawar cikin kyakkyawar niyya.

Tawagar da kasar Iran ta tura

Manyan jami’an Iran da ke halartar tattaunawar a Pakistan sun hada da:

  • Mohammad Bagher Ghalibaf: Shugaban majalisar dokokin Iran (Jagoran tawagar).
  • Abbas Araghchi: Ministan Harkokin Waje.
  • Reza Amiri Moghadam: Jakadan Iran a Pakistan.
  • Ali Akbar Ahmadian: Mamba a majalisar koli ta tsaron kasa.
  • Ali Bagheri Kani: Mataimaki a majalisar koli ta tsaron kasa.
  • Esmail Ahmadi Moghadam: Shugaban jami’ar tsaro ta kasa.
  • Naser Hemati: Gwamnan babban bankin Iran.
  • Kazim Gharibabadi: Mataimakin Ministan harkokin waje.
  • Majid Takht-e Ravanchi: Mataimakin Ministan harkokin wajen
  • Valiollah Nouri: Mataimakin Ministan harkokin waje.
  • Esmaeil Baghaei: Mataimakin Ministan harkokin waje kuma mai magana yawun bakin ma'aikatar.
  • Abolfazl Amouei: Mamba a majalisa
  • Mohammad Nabavian: Mamba a majalisa
Tawagar Iran ta isa Pakistan
Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf cikin jirgi yayin tafiya zuwa Pakistan Hoto: @MBGhalibaf
Source: Twitter

Kasashen Amurka da Iran za su tattauna

Kara karanta wannan

"Dole a cika su"; Iran ta gindaya sharudda 2 kafin fara tattaunawa da Amurka

Tattaunawar za ta zama mafi girma da Tehran da Washington suka taɓa yi tun bayan Juyin Juya Halin Musulunci na Iran a shekarar 1979.

Haka zalika, wannan ita ce tattaunawa ta farko a hukumance tun bayan shekarar 2015, lokacin da suka amince da yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Shugaba Trump ya soke wannan yarjejeniyar a shekarar 2018 lokacin wa’adinsa na farko.

A wannan shekarar ta 2018, tsohon jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya haramta tattaunawa kai tsaye da Amurka.

Idan za a iya tunawa, an kashe Khamenei a wani harin hadin gwiwa na Amurka da Isra’ila a farkon yakin makonni shida da suka gabata.

Shafin @pakistanfauj a X ya sanya bidiyon isar tawagar Iran a Pakistan.

Donald Trump ya yi barazana ga Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake yin barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Donald Trump ya yi barazanar komawa fagen daga da kasar Iran matukar tattaunawar sulhu da za a fara a Pakistan ba ta yi nasara ba.

Barazanar Trump na zuwa ne yayin da tawagar Amurka da ta kasar Musulunci ta Iran ke shirin fara tattaunawa a birnin Islamabad na Pakistan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng