Sabon Shirin Yaki: Amurka Ta Fadi Manyan Makaman da Ta Zargi China za Ta ba Iran
- Kasar Amurka ta zargi China da shirin tura makamai zuwa Iran yayin da aka kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da tattaunawa a Pakistan
- Wani rahoto da Amurka ta fitar ya nuna cewa kasar na zargin Iran za ta iya amfani da damar wajen kara adana makamai ko yaki ya barke a gaba
- A yau Asabar, 11 ga watan Afrilun 2026 za a tattauna tsakanin Iran da Amurka a kasar Pakistan a shirin tsayar da yakin da aka fara gaba daya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Rahotannin leƙen asirin Amurka sun nuna cewa China na shirin kai sababbin makaman kariyar sararin samaniya zuwa Iran cikin makonni masu zuwa.
Kasar ta ce wannan mataki na iya zama abin tada hankali, ganin cewa Beijing ta ce ita ce ta taimaka wajen jawo tsagaita wuta a yaƙi tsakanin Iran da Amurka a farkon wannan mako.

Kara karanta wannan
Ana batun sulhu da Iran, Shugaban Amurka zai ballo yakin da zai jefa kasashe a bala'i

Source: Facebook
Tashar CNN da ta wallafa sakon ta sanar da cewa mutane uku da suka san bayanan leƙen asirin Amurka na baya-bayan nan ne suka fada mata haka.
Yakin Iran: Korafin Amurka kan kasar China
Amurka ta yi korafi kan zargin taimaka wa Iran ne yayin da ake sa ran Shugaban Amurka Donald Trump zai ziyarci China a farkon wata mai zuwa domin ganawa da Shugaban China Xi Jinping.
Rahoton ya kuma nuna cewa Iran na iya amfani da tsagaita wuta a matsayin dama don sake cike gibin makamai da taimakon manyan abokan hulɗarta na ƙasashen waje.
Zargin tura wa Iran makaman China
Mutane biyu daga cikin majiyoyin sun shaida cewa akwai alamun cewa Beijing na ƙoƙarin bi ta wasu ƙasashe wajen jigilar makamai Iran domin ɓoye asalin inda suka fito.
Reuters ta ce majiyoyin sun ce tsarin da China ke shirin tura wa su ne makaman kariya daga jiragen sama da ake harbawa daga kafaɗa, waɗanda ake kira MANPADS.

Kara karanta wannan
Abu 1 da Shugaba Trump ya yi da ake tunanin zai zama alheri a tattaunawar Amurka da Iran
An bayyana cewa irin makaman ne suka zama babbar barazana ga jiragen saman sojin Amurka a lokacin yaƙin da ya ɗauki makonni biyar, kuma za su iya sake zama barazana idan tsagaita wutar ta rushe.
China ta karyata ikirarin Amurka
Wani mai magana da yawun ofishin jakadancin China a Washington ya karyata ikirarin Amurka, inda ba su taba ba wani bangare makami ba.
Ya ce:
“China ba ta taɓa bai wa kowanne ɓangare a rikici makamai ba; wannan bayanin ba gaskiya ba ne.”
“A matsayinta na babbar ƙasa, China na yin abi da ya kamata.
"Muna kira ga Amurka da ta guji zarge-zargen da ba su da tushe, haɗa labarai ba tare da hujja ba, da kuma ƙoƙarin tayar da hankali.”

Source: Getty Images
Ana so Trump ya ga likita a Amurka
A wani labarin, kun ji cewa wani dan majalisar Amurka ya yi kira a duba lafiyar shugaban kasa Donald Trump bayan dakatar da yaki da Iran.
Bayanan da Legit Hausa ta sun nuna cewa ya bayyana haka ne a cikin wata wasika da ya aika wa likitan shugaba Donald Trump.
'mnDan majalisar ya lissafo wasu kalamai da Donald Trump ya yi game da kai hare-hare Iran da barazanar shafe Tehran a doron kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng