"Ya na da Tabin Hankali," Yar majalisar Amurka Ta Yi Wasu Maganganu kan Trump

"Ya na da Tabin Hankali," Yar majalisar Amurka Ta Yi Wasu Maganganu kan Trump

  • Yassamin Ansari, 'yar majalisar wakilan Amurka, wadda ƴar asalin Iran ce, ta yi kaca kaca da Shugaba Donald Trump cikin kakkausan harshe
  • Ta ce Trump yana son ya zama "Sarki mai mulkin mallaka" maimakon zama shugaban ƙasa, kuma ya jefa rayuwar mutum miliyan 90 a hatsari
  • Ansari ta buƙaci a tsige Trump daga muƙaminsa saboda barazanar kisan kiyashi da kuma kai hare-hare kan asibitoci da makarantu a cikin kasar Iran

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka – Ƴar majalisar wakilan Amurka daga jihar Arizona, Yassamin Ansari, ta bayyana Shugaba Donald Trump a matsayin "mugun mutum" wanda yake son mayar da kansa "sarki mai mulkin mallaka" sakamakon yaƙin da ya yi da Iran.

Kalaman Ansari sun zo ne bayan da Trump ya yi barazanar shafe tarihin kasar Iran, kafin daga bisani ya janye tare da sanar da tsagaita buɗe wuta na tsawon mako biyu.

Kara karanta wannan

Iran ta dauki wani mataki da ya sa ta shiga gaban Amurka a shirin zaman sulhu a Pakistan

'Yar majalisar Amurka, Yassamin Ansari ta yi wa Donald Trump wankin babban bargo kan yaki da Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana jawabi a fadar White House da ke Washington D.C. Hoto: Drew Angerer/Getty Images
Source: Getty Images

"Ya na da matsalar ƙwaƙwalwa" - Ansari kan Trump

Yassamin Ansari, wadda ƴar asalin Iran ce, ta bayyana hakan ne a wata hira da jaridar The Guardian.

Ansari ta bayyana cewa mutane miliyan 90 a Iran sun shafe sa'o'i 24 mafi muni a rayuwarsu saboda fargabar harin nukiliya daga Amurka.

Ta jaddada cewa alkawuran da Trump ya yi na kisan kiyashi da cin zarafin bil'adama sun isa dalilin da zai sa majalisa ko mambobin gwamnatinsa su tsige shi daga muƙaminsa.

"Babu shakka a raina na san cewa ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa, kuma mugun mutum ne wanda bai damu da kowa ba sai kansa da iyalinsa," in ji Ansari.

Ta ƙara da cewa yayin da yake dakile talakawan Amurka daga samun ingantaccen tsarin kula da lafiyarsu, shi da iyalinsa suna samun biliyoyin daloli.

Fargabar jefa Amurka a yaki marar karshe

Ƴar majalisar ta nuna damuwarta kan yadda Trump ya saba alkawuransa na yaƙin neman zaɓe, inda ya yi alkawarin cewa ba zai jefa Amurka a yaƙe-yaƙe irin na Vietnam ko Iraq ba.

Kara karanta wannan

'Za mu ci gaba da kai hari,' Isra'ila ta sake tsokano Iran da ta kashe mutane a Lebanon

A wata hirar da ta yi da CNN, wadda ta wallafa bidiyon a shafinta na X, Ansari ta bayyana cewa a wannan zango na biyu na mulkinsa, Trump ya riga ya kai harin soja a ƙasashe bakwai, a lokuta daban daban.

"Abu ɗaya da ya sa wasu 'yan jam'iyyar Democrats suka ji daɗi lokacin da yake takara shi ne alkawarin kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe na har abada, amma a cikin watanni shida da suka gabata ya nuna cewa shi azzalumin shugaba ne, wanda yake son ya zama sarki mai cikakken ikon mulkin mallaka," in ji Ansari.
Yassamin Ansari ta ce akwai bukatar a tsige Donald Trump domin "ba shi da lafiyar kwakwalwa."
'Yar majalisar Amurka, Yassamin Ansari, ta na jawabi mambobin cibiyar Southwest Human Development a Amurka. Hoto: @RepYassAnsari
Source: Twitter

Zargin Trump da aikata laifukan yaƙi

Ansari ta kuma lissafa wasu matakai na Trump da ta kira haramtattu, kamar sace Nicolás Maduro a Venezuela, barazanar ƙwace yankin Greenland, da kuma lalata alaƙar Amurka da ƙungiyar NATO.

Ta bayyana cewa a ƙasar Iran, gwamnatin Trump ta riga ta aikata laifufukan yaƙi ta hanyar jefa bama-bamai da gangan kan makarantu, gadoji, da asibitoci.

A cewarta, Shugaba Trump ya zama babban hatsari ga Iran, Amurka, da ma duniya baki ɗaya, wanda hakan ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa kafin yaƙin ya sake rincibewa.

Kalli hirar Ansari a nan kasa:

Kara karanta wannan

Bayan cimma matsaya da Iran, sanarwar Shugaba Trump ta raba kan 'yan majalisar Amurka

An fara maganar tsige Trump

Tun da fari, mun ruwaito cewa, yayin da aka samu matsaya kan tsagaita wuta a yakin Iran da Amurka, 'yar majalisa, Ilhan Omar ta fara maganar tsige Donald Trump.

Ta mika bukatar gaggawa ga Shugaban majalisar Amurka tana neman a dawo zama domin tattauna batun tsige shi a hukumance.

Hakan na zuwa ne bayan barazanar shafe Iran a doron kasa da Trump ya yi, wanda ya sha suka daga ƙasashen duniya da wasu shugabanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com