Wata Sabuwa: Firaministan Isra'ila Ta Sake Dauko Rigima bayan Dakatar da Yakin Iran

Wata Sabuwa: Firaministan Isra'ila Ta Sake Dauko Rigima bayan Dakatar da Yakin Iran

  • Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya sanar da korar Spain tawagar hadin gwiwa ta aiwatar fa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
  • Netanyahu ya dauki wannan matakin ne domin hukunta Spain bisa abin da ya kira kim jinin manufofin kasar Yahudawa watau Isra'ila
  • Matakin ya zo ne bayan Spain ta yi kakkausar suka game da yakin Isra’ila da Iran, da kuma watsi da manufofin Isra’ila a Gaza da Yammacin Kogin Jordan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tel Aviv, Israel - Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya sake dauko wata rigimar yayin da ake shirye-shiryen fara tattaunawa tsakanin Amurka da Iran domin samar da zaman lafiya mai forewa.

A yau Juma'a, 10 ga watan Afrilu, 2026 ake sa ran tawagar Amurka da ta Iran za su fara tattaunawa a birnin Islamabad na kasar Pakistan domin warware duk wasu matsaloli da ke tsakaninsu.

Kara karanta wannan

'Za mu ci gaba da kai hari,' Isra'ila ta sake tsokano Iran da ta kashe mutane a Lebanon

Isra'ila.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana jawabi a taron kasa da kasa Hoto: @netanyahu
Source: Getty Images

Isra'ila ta kori Spain daga sulhun Gaza

Rahoton tashar Al-Jazeera ya nuna cewa yayin da ake shirin fara wannan zama na keke-da-keke, Firmainistan Isra'ila ya raba gari da Spain a yarjejeniyar zaman lafiya ta Gaza.

Netanyahu, ya sanar da cewa ya kori Spain daga wata tawagar hadin gwiwar soja da farar hula da aka kafa domin kula da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Wannan cibiyar dai wani bangare ne na shirin zaman lafiya mai sharudda 20 da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya tsara domin tabbatar da zaman lafiya a Gaza.

Dalilin Netanyahu na daukar matakin

Matakin ya zo ne bayan Spain ta yi kakkausar suka game da yakin Isra’ila da Iran, da kuma watsi da manufofin Isra’ila a Gaza da Yammacin Kogin Jordan.

Bugu da kari, Gwamnatin Spain ta yi Allah wadai da hare-haren bama-bamai da kuma mamayar Lebanon da Isra'ila ke yi, lamarin da ya harzuka jagoran kasar ta Yahudawa.

Kara karanta wannan

Awanni kafin shiga zauren tattaunawa, JD Vance ya fallasa shirin da Amurka ta yi wa Iran

A sanarwar da ya wallafa a shafin X, Netanyahu ya bayyana cewa:

“Isra’ila ba za ta yi shiru ba ga wadanda ke kai mana hari. Spain ta bata sunan jarumanmu, dakarun sojojin Isra'ila da muke alfahari da su.”
Pedro Sanchez.
Firaministan kasar Spain, Pedro Sanchez lokacin da ya kai wata ziyarar aiki kasar Ukraine Hoto: SOPA Images
Source: Getty Images

Ya kara da cewa ya bayar da umarni a cire wakilan Spain daga cibiyar da ke birnin Kiryat Gat, saboda Spain na yawan daukar matakai da ke adawa da Isra’ila.

“Ba zan lamunci wannan munafunci da gaba ba. Ba zan bari kowace kasa ta yi mana yakin diflomasiyya ba tare da ta fuskanci sakamako nan take ba,” in ji Netanyahu.

Isra'ila ta shirya fara tattaunawa da Lebanon

A wani rahoton, kun ji cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya sauya tunani bayan taso shi a gaba game da kai hare-haren rashin imani a kasar Lebanon.

Netanyahu ya bayyana cewa ya umarci majalisar ministoci ta fara tattaunawar zaman lafiya kai tsaye da Lebanon cikin gaggawa.

Ya ce wannan mataki ya biyo bayan bukatun da Lebanon ta dade tana yi na bude tattaunawa kai tsaye da Isra’ila domin samar da mafita mai dorewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262