Kasar Iran Ta Shirya wa Amurka da Isra’ila Tuggun da ba Zu Taba Mantawa ba
- Majalisar dokokin Iran ta gabatar da sabon daftarin doka domin tsara yadda za a sarrafa mashigar Hormuz wanda ake ya magana a kai
- Shugaban kwamitin ayyuka, Rezaei Kochi, ya ce daftarin ya haɗa da sababbin ƙa’idoji kan zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma tsarin karɓar kuɗin jangali
- Daftarin ya tanadi haramta wasu jirage, karɓar haraji da riyal, da kuma yadda za a raba kuɗaɗe don tsaro da walwalar al’umma
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Majalisar dokokin Iran ta fitar da wani sabon daftarin doka da ke nufin tsara yadda ƙasar za ta kula da mashigar Hormuz.
Ana sa ran za a tattauna tare da kaɗa ƙuri’a kan shi a mako mai zuwa domin samun mafita kan mashigar a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Facebook
Mashigar Hormuz: Majalisar Iran ta kawo kudiri

Kara karanta wannan
DSS ta gano tsohon 'dan majalisa da ya kada hantar Amurka da rashin tsaro a Najeriya
Shugaban kwamitin kula da ayyuka na majalisar, Mohammed Reza Rezaei Kochi, ya bayyana haka a yau Juma'a 10 ga watan Afrilun 2026, cewar BBC Hausa.
Kochi ya bayyana cewa daftarin ya ƙunshi sauye-sauye masu muhimmanci kan zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma tsarin kuɗaɗen da za a riƙa karɓa yayin da ake yakin Iran da Isra'ila.
Ya shaida cewa akwai kyakkyawan fata cewa dukkan ƴan majalisar za su amince da kudirin, kafin daga bisani a fara aiwatar da shi a hukumance.
A cikin daftarin, an tsara matakai guda biyar, ciki har da hana jiragen mai da ke da alaƙa da Amurka da Isra’ila wucewa ta mashigar Hormuz har abada.
Haka kuma, an tanadi karɓar kuɗin jangali daga jiragen ruwa domin kula da jagoranci da tsaro yayin da suke ratsawa, tare da tabbatar da aminci a wannan muhimmiyar hanya.
Bugu da ƙari, daftarin ya buƙaci duk jiragen ruwa su biya kuɗin ne da takardar kuɗin Iran ta riyal, a wani yunƙuri na ƙarfafa darajar kudin ƙasar.

Source: Getty Images
Sabon sunan da aka wajabta kan mashigar Hormuz
Har ila yau, an wajabta amfani da sunan “Mashigar Persia” a duk takardun jiragen ruwa da bayanan tafiya, maimakon wasu sunaye daban.
A ƙarshe, an tsara yadda za a raba kuɗaɗen da aka samu, inda kashi 30 za su tafi ga tsaro da soji, yayin da kashi 70 za su taimaka wajen inganta rayuwar jama’a.
Har ila yau, an wajabta amfani da sunan “Mashigar Persia” a duk takardun jiragen ruwa da bayanan tafiya, maimakon wasu sunaye daban, cewar Anadolu Ajansi.
A ƙarshe, an tsara yadda za a raba kuɗaɗen da aka samu, inda kashi 30 za su tafi ga tsaro da soji, yayin da kashi 70 za su taimaka wajen inganta rayuwar jama’a.
Iran ta yi wa Isra'ila illa
Mun ba ku labarin cewa kasar Iran ta bayyana irin illar da ta yi wa Isra'ila yayin ta ke ci gaba da hana wasu kasashe bi ta hanyar mashigar ruwan Hormuz.
Rundunar 'Islamic Revolutionary Guards Corps' da ake kira IRGC ta dauki alhakin kai hari kan wani jirgin ruwan Isra'ila.
Tashin hankalin yankin ya kara tsananta sakamakon rikicin Iran da Amurka da Isra’ila wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
Asali: Legit.ng
