Rikici Ya Tsananta: Harin Isra’ila kan Motocin Agaji Ya Girgiza Lebanon
- Rahotanni sun bayyana cewa dakarun IDF na kasar Isra'ila sun kara kai harin ce harin sama a kan motocin agajin gaggawa a Lebanon
- Bayan mummunan harin da ta kai Kudancin kasar, Isra’ila ta zargi kungiyar Hezbollah da amfani da motocin wajen aikin sojin da suke yi
- Lamarin ya kara dagula yanayin tsaro a yankin, a dai-dai lokacin da ake kokarin hada kan Amurka da Iran su zauna a teburin tattaunawa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Israel – Rahotannin da ke fitowa daga kasar Lebanon sun bayyana cewa wani hari ta sama da Isra’ila ta kai ya lalata wasu motocin daukar marasa lafiya da na kashe gobara a kudancin kasar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa harin ya auku ne a garin Deir Qanoun Ras al-Ain, inda aka ce an kai farmakin kai tsaye kan wadannan motocin da ake amfani da su wajen ceton rayuka.

Source: Twitter
Aljazeera ta wallafa cewa a cewar rahoton, motocin na kan aiki ne a lokacin da aka kai harin, lamarin da ya jawo fargaba da kuma jikkata wasu ma’aikatan agaji.
Harin Isra'ila ya salwantar da rayuka
First Post ta ruwaito cewa har yanzu ba a kai ga gano adadin mutanen da mummunan harin ya taba ba, duk da ana ci gaba da bincike.
Wannan hari ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da tashin hankali a yankin, wanda ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi a bangarori daban-daban.
Masu sa ido kan harkokin jin kai sun nuna damuwa kan yadda ake kai hari kan kayayyakin aikin agaji, suna mai cewa hakan na iya tauye kokarin ceto rayukan fararen hula da ke cikin hadari.
Har ila yau, sun jaddada cewa dole ne bangarorin da ke rikici su mutunta dokokin kasa da kasa da ke kare ma’aikatan jinya da motocin agaji a lokacin yaki.
Isra'ila ta kare kanta kan hare-hare
Kafin aukuwar wannan hari, rundunar sojin Isra’ila ta yi zargin cewa kungiyar Hezbollah na amfani da motocin ambulans wajen gudanar da ayyukan soja.
Sai dai kawo yanzu, babu wata hujja a fili da Isra’ila ta gabatar domin tabbatar da wannan ikirari da ta ke yi da har zai kare matakin kashe bayin Allah da ke aikin ceton rai.

Source: Getty Images
A gefe guda kuma, bangaren Lebanon da wasu kungiyoyi sun yi watsi da zargin, sun bayyana cewa ana amfani da shi ne wajen ba da uzuri ga hare-haren da ke shafar fararen hula.
Lamarin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin Isra’ila da Hezbollah, wanda ya riga ya janyo tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
Haka kuma ana kokarin sasanta Amurka da Isra'ila, daga cikin sharuddan da Iran ta ce za ta amince da su akwai tsagaita wuta na sa baba ta gani a Lebanon.
Netanyahu ya shiga matsala a Isra'ila
A baya mun wallafa cewa Wani 'dan jam'iyyar adawa a Isra'ila, Yair Lapid ya zargi Firaministan kasarsa, Benjamin Netanyahu da gazawa ta fannin siyasa, lamarin da ya ce ya jefa su a cikin wani hali.
Ya bayyana haka ne a lokacin da Isra'ila ke ci gaba da take yarjeniyoyin da aka kulla wajen wanzar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ta hanyar kai hare-hare Lebanon da wasu yankunan da Falasdinu.
Lapid ya gargadi cewa gyaran barnar siyasa da Netanyahu ya jawo wa kasarsa zai dauki tsawon shekaru kafin a samu gyara, inda ya bayyana cewa ba a taba jefa Isra'ila a cikin hali irin wannan ba.
Asali: Legit.ng


