Duk da Fargabar Iran ba za Ta Halarta ba, Ana Shirin Zaman Sulhu da Amurka
- Kasar Pakistan ta fara shirin karɓar tawagogin Amurka da Daular Musulunci ta Iran domin tattaunawa mai muhimmanci a Islamabad
- Sai dai akwai fargaba a kan yiwuwar Iran na iya janye halartar taron tun bayan da Isra'ila ta yi fatali da wani sashe na yarjejeniyar da aka cimma
- Wani bangare da Amurka da Isra'ila suka dage a kai shi ne babu inda aka yi maganar daina kashe bayin Allah da Yahudawa ke yi a Lebanon
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Islamabad, Pakistan – Kasar Pakistan na shirin karɓar tawagogi daga Amurka da Iran domin gudanar da muhimman tattaunawa a babban birninta, Islamabad.
Pakistan na wannan shiri duk da cewa akwai shakku kan halartar Iran sakamakon sababbin hare-haren Isra’ila a Lebanon da suka jefa yarjejeniyar tsagaita wuta cikin haɗari.

Kara karanta wannan
Kasar Iran ta amince za ta tura tawaga, ta bayyana abin da za ta gabatar ga Amurka

Source: Twitter
Aljazeera ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa za a tattauna batutuwa masu matuƙar muhimmanci, ciki har da shirin nukiliyar Iran da kuma zirga-zirgar kasuwanci ta mashigar ruwa ta Hormuz.
Za a zauna kan sulhun Iran da Amurka
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa duk da shirye-shiryen tsaro da aka ƙara a Islamabad, Iran ta bayyana cewa halartar ta na iya rataya ne kan dakatar da hare-haren Isra’ila a Lebanon.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya ce tattaunawar za ta yiwu ne kawai idan Amurka ta mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta a dukkannin bangarori.
Sai dai rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran ta nuna goyon bayanta ga tsagaita wuta, tana mai cewa ba ta kai wani hari ba tun bayan fara yarjejeniyar.
Amurka za ta gana da Isra'ila
A gefe guda, an tabbatar da cewa Amurka za ta karɓi wata ganawa a mako mai zuwa tsakanin Isra’ila da Lebanon domin tattauna batun tsagaita wuta.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Amurka ta karya sharudda 3 daga cikin yarjejeniyar sulhu da kasar Iran
Duk da haka, babu wata sanarwa kai tsaye daga bangarorin biyu da ta tabbatar da wannan ganawa da ake sa ran zai taimak wajen kare asarar rayuka.

Source: UGC
Hare-haren Isra’ila mafi muni a Lebanon tun farkon shiga Hezbollah cikin rikicin Gabas ta Tsakiya sun kashe daruruwan mutane, lamarin da ya girgiza yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran.
Gwamnatin Lebanon ta bayyana cewa ba za ta shiga wata tattaunawa da Isra’ila ba sai an samu tsagaita wuta.
Ministan Pakistan ya yi kaca-kaca da Isra'ila
A baya, mun wallafa cewa takaddama ta barke tsakanin Pakistan da Isra'ila bayan ministan tsaro, Khawaja Asify ya zargi kasar Isra'ila da haddasa rikici a fadin duniya tare da zama annoba.
Hakan na zuwa ne yayin da aka tsagaita wuta a yakin Iran da Amurka kuma aka fara shirin tattaunawa tsakanin kasashen a Pakitsan, inda ita kuma Isra'ila ta ci gaba da kai hari Lebanon.
Ministan tsaron Pakistan, Khawaja Asif ya yi magana ne yayin da Benjamin Netanyahu ke luguden wuta a Lebanon duk da tsagaita wuta lamarin da ya zama mafi muni a harin da aka kai kasar.
Asali: Legit.ng