Ministan Pakistan Ya Yi Kaca Kaca da Isra'ila kan Zubar da Jini a Duniya

Ministan Pakistan Ya Yi Kaca Kaca da Isra'ila kan Zubar da Jini a Duniya

  • Takaddama ta barke tsakanin Pakistan da Isra'ila bayan Ministan tsaro, Khawaja Asify ya zargi Tel Aviv da haddasa rikici a fadin duniya
  • Hakan na zuwa ne yayin da aka tsagaita wuta a yakin Iran da Amurka kuma aka fara shirin tattaunawa tsakanin kasashen a Pakitsan
  • Ministan tsaron Pakistan, Khawaja Asif ya yi magana ne yayin da Benjamin Netanyahu ke luguden wuta a Lebanon duk da tsagaita wuta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Pakisatan - Ministan tsaron Pakistan, Khawaja Asif, ya bayyana Isra’ila a matsayin matsala ga bil’adama a cikin wani saƙo da ya fitar a ranar Alhamis wanda daga baya aka goge.

Khawaja Asif ya yi magana mai zafi game da Isra'ila, inda ya bayyana cewa yana fatan waɗanda suka kafa ta za su kasance cikin wadanda za a kona a lahira.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta amince za ta tura tawaga, ta bayyana abin da za ta gabatar ga Amurka

Khawaja Asif a wajen wani taro
Ministan Pakistan tsaron Pakistan, Khawaja Asif a wajen taro a China. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Jerussalem Post ya nuna cewa kalaman nasa sun zo ne a lokacin da Islamabad ke ƙoƙarin taka rawar diflomasiyya domin dakile rikicin Gabas ta Tsakiya.

Pakistan ta fito fili tana kira da a kawo ƙarshen hare-haren Isra’ila a Lebanon, yayin da kuma take shirin karɓar baƙuncin tattaunawar diflomasiyya kan yaƙin Iran a Islamabad.

Maganar ministan Pakistan kan Isra'ila

Rahotanni sun ce Firaministan Lebanon, Nawaf Salam, ya nemi goyon bayan Pakistan domin a kawo ƙarshen hare-haren Isra'ila a kasar.

Haka kuma, an sa ran wata tawagar Iran za ta isa Islamabad domin tattaunawa kan rikicin domin kawo zaman lafiya a yankin baki daya.

Ana tsaka da haka ne Asif ya rubuta cewa:

“Isra’ila muguwa ce kuma ta zama matsala ga bil’adama.’
"Yayin da ake maganar gudanar da tattaunawar zaman lafiya a Islamabad, ana aiwatar da ‘kisan kare dangi’ a Lebanon,”

The Economics Times ta wallafa cewa ya ƙara da cewa Isra'ila ta kashe fararen hula marasa laifi:

Kara karanta wannan

Netanyahu ya fara shiga matsala a Isra'ila ana cigaba da yakar Iran da makwabtan kasashe

“Ta fara da Gaza, sannan ta wuce Iran, yanzu kuma tana Lebanon,”
Wajen da Isra'ila ta kai hari a Lebanon
Wani gini da Isra'ila ta rusa a Lebanon. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Karin maganar Asif kan Isra'ila

A cikin saƙon, Asif ya ce yana fatan waɗanda suka kafa “wannan ƙasa mai kama da cutar kansa” a ƙasar Falasdinu “domin janye Yahudawa daga Turai” za su “ƙone a wuta.”

A baya ma, Asif ya yi amfani da kalamai masu tsauri kan Isra’ila. A watan Janairun 2026, ya ce Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ne “mafi girman mai laifi,.

Ya kuma yi kira da a kama shi a kai shi gaban kotu, yana mai ba da shawarar cewa Turkiyya za ta iya ɗaukar wannan mataki.

Kasar Faransa ta yi tir da Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya sanar da cewa hare-haren Isra'ila a Lebanon abin Allah wadai ne.

Ya bayyana haka ne bayan Benjamin Netanyahu ya kaddamar munanan hare-haren da suka jawo asarar rayuka sama da 200 a Lebanon.

Macron ya sanar a cewa ya yi magana da kasashen duniya da dama, inda ya ce ya zama wajibi Isra'ila ta dakatar da kai hari kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng