Mai Dakin Trump Ta Yi Maganganu da Dama, Ta Fadi Alakarta da Epstein
- Uwargidan shugaban Amurka, Melania Trump ta fito fili ta yi magana kan yada rahoto game da alaka da Jeffrey Epstein
- Ta bayyana cewa tana tare da lauyoyinta wajen yakar abin da ta kira 'zarge-zargen banza marasa tushe'
- Jawabin nata ya sake dawo da batun Epstein cikin siyasa, yayin da ‘yan Democrat suka goyi bayan bukatar gudanar da sauraron jama’a
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Uwargidan shugaban Amurka, Melania Trump, ta yi karin haske game da zargin alaka da Jeffrey Epstein.
Melania ta musanta duk wata alaka da marigayi attajiri Epstein, tana mai cewa dukkan labaran da ake yadawa game da ita karya ne.

Source: UGC
Epstein: Matar Trump ta fusata kan yi mata sharri
A cikin wata sanarwa da ta karanta a fadar White House, ta bayyana zarge-zargen a matsayin “kage-kage marasa tushe,” tana mai cewa ana kokarin bata mata suna ne ba tare da hujja ba, cewar AP News.
Ta ce ita da lauyoyinta suna kokarin dakile irin wadannan zarge-zarge, tare da jaddada cewa ba ta da wata alaka da Epstein ko laifukan da aka same shi da su.
Melania Trump ta kara da cewa:
“Karyar da ake danganta ni da Epstein dole ta kare yanzu. Wadanda ke yada wannan labari ba su da da’a ko mutunci.”

Source: Twitter
Batun Epstein ya sake dawo wa a Amurka
Wannan jawabi ya zo ne a lokacin da gwamnatin mijinta, Donald Trump, ke kokarin kaucewa ce-ce-ku-ce da suka shafi Epstein, musamman yayin da rikicin Iran ya mamaye hankalin gwamnati.
Sai dai furucin nata ya sake jawo hankalin jama’a kan batun, duk da cewa shugaban ya bukaci a wuce wannan batu.
Ta kuma bukaci majalisar dokokin Amurka ta gudanar da sauraron jama’a inda wadanda Jeffrey Epstein ya cutar za su samu damar bayyana labarinsu a fili.
A cewarta, kowace mace tana da hakkin fadin abin da ya same ta idan tana so, domin a gano gaskiya da tabbatar da adalci, cewar The Guardian.
‘Yan jam’iyyar Democrat sun nuna goyon baya ga wannan kira, inda suka bukaci a gaggauta shirya zaman sauraron jama’a kan lamarin.
Melania Trump ta bayyana cewa ba kawance ne tsakaninta da Epstein ko abokiyar aikinsa Ghislaine Maxwell ba, sai dai sun taba haduwa a wasu taruka na zamantakewa kawai.
A cikin bayaninta, ta jaddada cewa Epstein bai hada ta da mijinta ba, tana mai cewa ta hadu da Donald Trump ne a wani biki a New York tun shekarar 1998.
An 'gano' alakar Epstein da Boko Haram
Mun ba ku labarin cewa wani sabon bincike ya danganta marigayi Jeffrey Epstein da tsohon Firaministan Isra’ila, Ehud Barak da Boko Haram.
Rahoton ya ce an yi amfani da tattaunawar tashoshin jiragen ruwa a Lagos da Badagry, da kuma fasahar tsaro, domin samun moriyar kasuwanci.
Binciken ya yi zargin cewa hanyoyin tsaro da jarin da aka zuba sun bai wa bangarorin damar cin gajiyar rashin zaman lafiyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

