Netanyahu Ya Sauko bayan Ya Ji Wuya, Ya Shirya Tattaunawa domin Tsagaita Wuta

Netanyahu Ya Sauko bayan Ya Ji Wuya, Ya Shirya Tattaunawa domin Tsagaita Wuta

  • Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya sauko bayan taso shi a gaba game da kai hari a kasar Lebanon
  • Netanyahu ya ce ya umurci fara tattaunawar zaman lafiya da Lebanon cikin gaggawa, ciki har da batun kwance damarar kungiyar Hezbollah
  • Ya bayyana cewa Lebanon ta dade tana neman tattaunawa kai tsaye, yayin da Shugaban kasar Lebanon ya ce tsagaita wuta ne mafita kafin fara sulhu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya sanar da maganar tattaunawa da kasar Lebanon a Gabas ta Tsakiya.

Netanyahu ya bayyana cewa ya umarci majalisar ministoci ta fara tattaunawar zaman lafiya kai tsaye da Lebanon cikin gaggawa.

Netanyahu ya shirya tattaunawar zaman lafiya da Lebanon
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana jawabi a birnin Tel Aviv. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Netanyahu ya magantu kan tattaunawar tsagaita wuta

Ya ce wannan mataki ya biyo bayan bukatun da Lebanon ta dade tana yi na bude tattaunawa kai tsaye da Isra’ila domin samar da mafita mai dorewa, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta amince za ta tura tawaga, ta bayyana abin da za ta gabatar ga Amurka

A cewarsa, tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan kwance damarar kungiyar Hezbollah tare da kokarin kafa dangantakar zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.

Ya ce:

“A bisa la’akari da maimaitattun bukatun da Lebanon ke yi na bude tattaunawa kai tsaye da Isra’ila, na umurci majalisar ministoci jiya da ta fara tattaunawa kai tsaye da Lebanon cikin gaggawa.
“Wannan tattaunawa za ta mayar da hankali ne kan kwance damarar kungiyar Hezbollah da kuma kafa dangantakar zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Lebanon.”

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Gwamnatin Lebanon ba ta mayar da martani kai tsaye ga kalaman Benjamin Netanyahu ba dangane da wannan sabon yunkurin sulhu.

Isra'ila ta amince da tattaunawa a Lebanon
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Gil Cohen-Magen.
Source: Getty Images

Isra'ila ta fadi mafita tsakaninta da Lebanon

Sa’a guda kafin bayanin Netanyahu, Shugaban Lebanon, Joseph Aoun, ya ce mafita daya tilo ita ce tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon sannan a fara tattaunawa.

Ya kara da cewa yana aiki kan hanyoyin diflomasiyya da ke samun karbuwa daga kasashen duniya domin kawo karshen rikicin da ke addabar yankin.

Isra’ila ta kaddamar da sababbin hare-hare kan Hezbollah bayan kungiyar mai goyon bayan Iran ta fara harba makamai kan Isra’ila tun ranar 2 ga Maris, 2026, kamar yadda Reuters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Amurka ta karya sharudda 3 daga cikin yarjejeniyar sulhu da kasar Iran

Hukumomin Lebanon sun ce hare-haren sun kashe kusan mutane 1,700 tare da tilasta wa sama da mutane miliyan daya barin gidajensu saboda tashin hankali.

Majiyoyi sun ce akalla mayakan Hezbollah 400 ne suka mutu, yayin da kungiyar ta ci gaba da harba rokoki da jiragen marasa matuki kan Isra’ila.

Isra'ila ta hallaka liman a Lebanon

A wani labarin, an ji cewa majiyoyi sun bayyana cewa wani harin sama da Isra’ila ta kai a kudancin Lebanon ya yi sanadin mutuwar ‘yan mata uku daga gida daya.

Harin ya kuma haddasa mutuwar fitaccen limamin Lebanon, Sadiq al-Nabulsi, yayin da Hezbollah ta yi barazanar daukar fansa.

Rikicin kan iyakar kasashen biyu na ci gaba da tsananta, inda dubban mutane ke tserewa daga gidajensu bayan hare-haren da ake kai wa a kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.