A Karon Farko, Saudiyya Ta Yi Magana Mai Muhimmanci da Kasar Iran bayan Tsagaita Wuta

A Karon Farko, Saudiyya Ta Yi Magana Mai Muhimmanci da Kasar Iran bayan Tsagaita Wuta

  • Saudiyya da Iran sun yi tattaunawa ta farko tun bayan barkewar yaki tsakanin Jamhuriyar Musulunci da Amurka/Isra'ila
  • Wannan tattaunawa na zuwa ne kasa da kwanaki biyu bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da abokan gabarta
  • Ministan harkokin wajen Saudi, Faisal bin Farhan Al-Saud ya tattauna da takwarorinsa na kasashe da dama a Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudi Arabia - Ministan harkokin wajen Saudiyya, Faisal bin Farhan Al Saud, ya yi wata muhimmiyar waya da takwaransa na kasar musulunci ta Iran, Abbas Araghchi.

Wannan tattaunawa dai wani mataki ne da ke nuna kokarin da kasashen ke yi domin kawar da duk wani tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya musamman bayan tsagaita wuta.

Faisal bin Farhan Al Saud
Ministan harkokin wajen Saudiya, Faisal bin Farhan Al Saud a taron ministoci a birnin Riyadh Hoto: Fayez Nureldine
Source: Getty Images

NBC News ta ce wannan ita ce hulɗar farko a hukumance tsakanin kasashen biyu tun bayan hare-haren da Iran ta kai wa kasashen yankin Gulf a matsayin martani ga hare-haren Amurka da Isra’ila.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Amurka ta karya sharudda 3 daga cikin yarjejeniyar sulhu da kasar Iran

Ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta tabbatar da hakan a wata gajeruwar sanarwa da ta wallafa a shafin X yau Alhamis.

Abin da Saudiyya ta tattauna da Iran

A cewar Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya, tattaunawar ta mayar da hankali ne kan duba halin da ake ciki a yankin, lalubo hanyoyin rage zafin rikici da kuma kokarin dawo da tsaro da kwanciyar hankali.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan sanar da tsagaita wuta na makonni biyu tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran.

Saudiyya ta tattauna da wasu kasashe

Baya ga Iran, Ministan Saudiyya ya kuma yi tattaunawa da wasu manyan jami’an kasashen yankin, ciki har da Firaminista kuma Ministan Harkokin Wajen Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani.

Sauran wadanda ya yi magana da su sun hada Ministan Harkokin Wajen Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan, Ministan Harkokin Wajen Jordan, Ayman Safadi da takwaransu na Turkiyya, Hakan Fidan.

Dukkan bangarorin sun yi maraba da duk wani yunkuri da zai kawo zaman lafiya da daidaito a yankin.

Goyon bayan tsagaita wuta

Kara karanta wannan

Ba boye boye, an ji abin da Saudiyya da wasu kasashe suka yi yayin sulhunta Amurka da Iran

A baya, Saudiyya ta nuna goyon bayanta ga yarjejeniyar tsagaita wuta da Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, suka sanar.

Haka kuma, Saudiyya ta yaba da kokarin hafsan sojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, wajen taimakawa cimma yarjejeniyar.

Sai dai duk da wannan cigaba, akwai damuwa kan karya yarjejeniyar tsagaita wuta, musamman a Lebanon.

Ministan Iran.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi a wani taro a birnin Riyadh Hoto: Karim Jaafar
Source: Getty Images

A wata tattaunawa daban, Ministan harkokin wajen Pakistan, Ishaq Dar, da takwaransa na Saudiyya sun nuna damuwa kan hakan, suna mai kira da a mutunta yarjejeniyar domin tabbatar da dorewar zaman lafiya.

Iran ta yi barazanar kai hari Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa Iran ta dauki zafi kan hare-haren da Isra'ila ta sake kai wa kasar Lebanon bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Gabas ta Tsakiya.

Iran ta ce za ta janye daga yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka idan har Isra'ila ta ci gaba da keta yarjejeniyar ta hanyar kai hare-hare a kasar Lebanon.

Majiya ta ce dakatar da fada a kowane bangare, ciki har da yakar kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Lebanon, na cikin tsarin tsagaita wutar da aka amince da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262