Kashe Khamenei da Manyan Abubuwa 10 da Suka Faru a Yakin Iran da Amurka a Kwana 40
Wasu muhimman abubuwa da suka ja hankalin duniya sun faru tun bayan fara yakin Iran da Amurka/Isra'ila a ranar 28 ga Fabrairu zuwa ranar 8 ga Afrilun 2026.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - A ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026 kasashen Amurka da Isra'ila suka kaddamar da hare-hare kan Iran, lamarin da ya jawo barkewar yaki a Gabas ta Tsakiya.
Kasar Pakistan ta shiga tsakani wajen ganin a tsayar da yakin na mako biyu a ranar Talata, 8 ga watan Afrilun 2026, bayan kwana 40 ana fafatawa.

Source: Getty Images
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku wasu muhimman abubuwa da suka faru a lokacin yakin da ya jawo asarar dukiya da rayuka.
1. Kashe Ayatollah Ali Khamanei
Ranar farko da aka kaddamar da yakin, Isra'ila da Amurka sun hada kai sun kai munanan hare-hare Iran a daidai lokacin da ake tattaunawa.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei da wasu 'yan uwansa ciki har da matar shi da ta rasu daga baya.

Source: Getty Images
2. Kashe wasu jagororin Iran
Bayan kashe Ayatollah Khamenei, Iran ta cigaba da kai hare-haren ramuwar gayya, inda Amurka da Isra'ila suka cigaba da kai hari su ma.
Hare-haren Amurka/Isra'ila sun kashe wasu daga cikin jagororin Tehran, ciki har da sakataren majalisar tsaron Iran, Ali Larijani.

Source: Twitter
Reuters ta rahoto cewa an kashe kwamandan IRGC, Mohammad Pakpour tare da ministan leken asirin Iran, Esmail Khatib a hare-haren da wasu manyan jami'ai.
3. Kashe sojojin Amurka
Wani abin da ya dauki hankali a yakin shi ne yadda dakarun Iran suka rika kashe wasu daga cikin sojojin Amurka a Saudiyya da wasu kasashe.
Rahoton Military Times ya nuna cewa a cikin kwanaki 40 tun bayan fara yakin, sojojin Amurka 13 sun mutu, yayin da 381 suka jikkata.
Farmakin da harbo jiragen sojojin Amurka a kasashen Gabas ta Tsakiya da makalewar sojan da aka kakkabo jirginsa a Tehran ya dauki hankali sosai.

Source: Facebook
4. Nada Mojtaba Khamenei
Bayan kashe Ayatollah Ali Khamenei, jama'a da dama na jiran ganin wanda zai gaje shi wajen jagorantar kasar Iran a lokacin yakin.
Kwanaki kadan bayan haka, gwamnatin Iran ta sanar da nada dan shi, Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin kasar.

Source: Getty Images
5. Maganganun Trump kan cin nasara
Daga cikin abubuwan da suka faru da suka dauki hankali akwai ikirarin shugaban Amurka da ya ke yi cewa ya gama rusa kasar Iran.
Abin da ya sanya lamarin ya ja hankali shi ne yadda Iran ke cigaba da harba makamai da kuma yadda Trump ke neman taimakon kasashen NATO duk da ikirarin cewa ya gama da Tehran.

Source: Facebook
6. Rufe mashigar Hormuz
Wani babban al'amari da ya ja hankalin duniya shi ne rufe mashigar Hormuz da Iran ta yi bayan fara yakin, lamarin da ya jawo tashin farashin mai a duniya.
Trump ya nemi kasashe su hadu a bude mashigar amma suka ki, inda da dama suka nemi a yi amfani da diflomasiyya maimakon nuna karfin soja.

Source: Getty Images
7. Jita-jitar mutuwar Netanyahu
Sakamakon wasu hare-hare da Iran ta kai Tel Aviv, an yada jita-jitar cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya mutu.
Duk da ya fito ya yi bidiyon cewa yana raye, jita-jitar ta ki karewa, hakan na ya jawo maganganu da zargin cewa da fasahar AI aka yi bidiyon.

Source: Getty Images
8. Ajiye aikin jami'in Trump
BBC ta rahoto cewa babban jami’in yaki da ta’addanci na Donald Trump wato Joe Kent ya yi murabus sakamakon yakin Iran, yana kira shugaban kasar ya sake nazari.
A cikin wata wasika da ya fitar, Joe Kent, ya ce:
“Iran ba ta zama barazana kai tsaye ba ga Amurka.”
Kuma ya yi zargin cewa gwamnatin Trump ta:
“Fara yakin ne sakamakon matsin lamba daga Isra’ila.”

Source: Twitter
9. Zanga zanga a Iran da Amurka
Yayin da ake cigaba da yakin, miliyoyin mutane sun fito kan tituna a Amurka suna Allah wadai da matakan da Donald Trump ya dauka na fara yakin.

Kara karanta wannan
Babu sulhu da Iran, Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a garuruwa 12 na kasar Musulunci
A gefe guda kuma an hango 'yan Iran da dama suna nuna goyon baya da kasarsu, ciki har da taruwa a wuraren da Donald Trump ya ce zai kai hari.

Source: Getty Images
10. Barazanar shafe Iran a duniya
Wani abu da ya dauki hankalin al'ummar duniya a yakin shi ne barazanar Donald Trump na cewa zai shafe Iran a doron kasa idan bata bude Hormuz ba.
Al-Jazeera ra rahoto cewa barazanar Trump ta sanya wasu shugabanni a duniya, ciki har da Fafaroma Leo kira da a kai zuciya nesa da komawa teburin sulhu.

Source: Getty Images
Iran da Amurka za su zauna
A wani labarin, mun kawo muku cewa bayan yarda da tsagaita wuta na mako biyu, wakilan Amurka da Iran za su tattauna a Pakistan.
Firaministan Pakistan ya sanar da cewa wakilan kasashen za su zauna a kasar shi a ranar Juma'a, 10 ga watan Afrilun 2026.
Kasashe da dama sun yaba da matakin da Pakistan ta dauka na jawo tsagaita wutar, inda ake fatan hakan zai kawo karshen yakin gaba daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


