Ana Wata ga Wata: Amurka Ta Karya Sharudda 3 daga cikin Yarjejeniyar Sulhu da Kasar Iran

Ana Wata ga Wata: Amurka Ta Karya Sharudda 3 daga cikin Yarjejeniyar Sulhu da Kasar Iran

  • Shugaban Majalisar Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf ya lissafa sharudda uku da yake zargin Amurka ta karya a yarjejeniyar tsagaita wuta
  • Ya ce wannan ne misalin mai sauki game da dalilin da ya sa kasar Musulunci ta Iran ba ta yarda da alkawurran Amurka
  • Duk da wadannan zarge-zarge, Ghalibaf bai bayyana a fili ko Iran ta janye daga yarjejeniyar tsagaita wuta ba ko za ta halarci zaman da aka shirya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya zargi Amurka da karya wasu muhimman sharudda uku daga ciki 10 da kasar ta gabatar domin tattaunawa.

Wannan zargi dai na zuwa ne kasa da kwana guda bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin da ke yaki a Gabas ta Tsakiya.

Khamenei.
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Tashar NBC News ta ruwaito cewa hare-haren da Isra'ila ta kai a yau Laraba kan kasar Lebanon sun fusata Iran, inda ta yi baranzanar daukar mataki idan Amurka ba ta tsawatar mata ba.

Kara karanta wannan

Tun ba a je ko'ina ba, Shugaba Trump ya canza tsarin tattaunawar Amurka da kasar Iran

Sharuddan da ake zargin Amurka ta karya

Abubuwan da shugaban majalisar Iran ke zargin Amurka ta karya a sharuddan yarjejeniyar tsagaita wutar sun hada da;

1. Ci gaba da kai hare-hare a Lebanon

2. Gano jirgin sama maras matuki (drone) a sararin samaniyar Iran

3. Yunkurin hana Iran ci gaba da shirinta na sarrafa sinadarin uranium

Ghalibaf ya bayyana cewa irin wannan hali na kara tabbatar da rashin amincewar da Iran ke yi wa Amurka tun shekaru da dama da suka shige.

Ya rubuta a shafinsa na X cewa:

“Wannan rashin amincewa da muke da shi kan Amurka ya samo asali ne daga yadda take karya alkawura akai-akai, kuma abin takaici, hakan ya sake faruwa.”

Rikicin Lebanon ya kara dagulewa

A halin da ake ciki, shugabannin Amurka da Isra’ila, Donald Trump da Benjamin Netanyahu, sun jaddada cewa Lebanon ba ta cikin yarjejeniyar tsagaita wuta, abin da ya sa aka ci gaba da kai hare-hare a can.

Kara karanta wannan

Ba boye boye, an ji abin da Saudiyya da wasu kasashe suka yi yayin sulhunta Amurka da Iran

Wannan mataki ya kara dagula lamarin, domin Iran na kallon hakan a matsayin karya yarjejeniyar da aka cimma, in ji rahoton Al-Jazeera.

Takaddama kan shirin uranium na Iran

Fadar White House ta kuma bayyana cewa dole ne Iran ta dakatar da shirinta na sarrafa uranium, wanda ke daya daga cikin manyan abubuwan da ake takaddama a kai.

Ghalibaf ya ce:

“Wannan tushen tattaunawa da aka ce zai yiwu, an riga an karya shi tun kafin a fara.”

Ya kara da cewa a irin wannan yanayi, tsagaita wuta ko shiga tattaunawa tsakanin bangarorin biyu ba abu ne mai ma’ana ba.

Shugaban Amurka.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: @RealDonaldTrump
Source: Twitter

Duk da wadannan zarge-zarge, Ghalibaf bai bayyana a fili ko Iran ta janye daga yarjejeniyar tsagaita wuta ba, ko za ta ci gaba da shirin tattaunawa da Amurka a kasar Pakistan kamar yadda aka tsara.

Iran ta bai wa Amurka zabi 2

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin kasar Iran ta bukaci Amurka ta zabi daya tsakanin tsagaita wuta da ci gaba da kai wa juna hare-hare ta hannun Isra'ila.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta bayyana matsayarta kan sulhu da Iran, ta fadi kasar da za ta afkawa

Ministan Harkokin Waje, Abbas Araghchi ya nuna bacin ran Iran kan hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa kasar Lebanon duk da an tsagaita wuta.

Ya ce a halin yanzu duniya za ta zuba ido ta ga ko Amurka za ta yi biyayya ga sharuddan da aka amince da su na tsagaita wuta ko kuma a'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262