Yaki na Neman Dawowa Danye, Kasar Musulunci Ta Iran Ta Bai Wa Amurka Zabi 2

Yaki na Neman Dawowa Danye, Kasar Musulunci Ta Iran Ta Bai Wa Amurka Zabi 2

  • Gwamnatin kasar Iran ta bukaci Amurka ta zabi daya tsakanin tsagaita wuta da ci gaba da kai wa juna hare-hare ta hannun Isra'ila
  • Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan yayin da yake martani kan hare-haren da Isra'ila ta sake kai wa kasar Lebanon
  • Ya ce a halin yanzu duniya za ta zuba ido ta ga ko Amurka za ta yi biyayya ga sharuddan da aka amince da su na tsagaita wuta ko kuma a'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Ministan Harkokin Waje kuma Babban jami'in diflomasiyyar Iran, Abbas Araghchi ya bayyana damuwa kan hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa kasar Lebanon duk da an tsagaita wuta .

Araghchi ya yi gargadin cewa dole ne Amurka ta zabi daya daga cikin biyu: ci gaba da yaki ta hanyar Isra'ila ko kuma tsagaita bude wuta da nufin dawo da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Amurka ta karya sharudda 3 daga cikin yarjejeniyar sulhu da kasar Iran

Abbas Araghchi.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi yana jawabi a wurin taro a birnin Doha Hoto: Karim Jaafar
Source: Getty Images

Kasar Iran ta bai wa Amurka zabi 2

Tsahar Al-Jazeera ta ruwaito cewa ministan ya ba Amurka wannan zabi guda biyu ne saboda abin da Iran ta kira keta sharuddan tsagaita wuta da Isra'ila ke yi.

"Sharuddan tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka a bayyane suke: Dole ne Amurka ta zabi ko dai tsagaita wuta ko kuma ci gaba da yaki ta hannun Isra'ila, zabin guda biyu ba za su taba zama tare ba.
"Duniya tana ganin kisan kiyashin da ake yi a Lebanon. Yanzu sauran mu ga matakin da Amurka za ta dauka, a halin yanzu al'ummar duniya sun zuba ido su gani ko wannan kasa za ta cika alkawuranta ko a'a."

Pakistan ta nemi a mutunta yarjejeniya

Bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, Gwamnatin Pakistan ta hannun Ministan tsare-tsare, Ahsan Iqbal Chaudhary, ta ce ya zama wajibi kowace kasa ta bi duka sharuddan da aka gindaya.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta gano matsala a sharuddan tsagaita wuta, ta shirya koya wa Isra'ila darasi

Ministan ya jaddada cewa Pakistan ta yi amanna cewa dole ne dukkan bangarori su bi yarjejeniyar tsagaita wuta kuma Idan aka kawo cikas ga tsarin samar da zaman lafiya, hakan ba zai amfani kowane bangare ba.

Netanyahu da Trump.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da Shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: Joe Raedle
Source: UGC

Iran ta fusata da ayyukan Isra'ila

Wata majiyar tsaro ta shaida wa CBS News cewa Iran tana duba yuwuwar hukunta Isra'ila kan wadannan jerin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta yi.

Da yake martani kan lamarin, babban jami'in diflomasiyyar Iran, Abbas Araghchi ya ba Amurka zabi biyu, ko dai tsagaita wuta da ya fara aiki jiya Talata ko kuma a ci gaba da yaki ta hannun Isra'ila.

Trump ya canza dabara kan tsagaita wuta

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya nuna damuwa kan jerin sharuddan da ake yadawa tare da jingina su ga yarjejeniyar tsagaita wuta ta Amurka da Iran.

Hakan na zuwa ne kasa da awanni 24 bayan Trump ya sanar da cewa Amurka ta fara samun daidaito da Iran, kuma sun amince da dakatar da kai wa juna hare-hare na tsawon mako biyu.

Sakamakon abin da ya kira karairayin da ake yadawa, Trump ya ce Amurka za ta tattauna kan abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa a asirce

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262