Bayan Cimma Matsaya da Iran, Sanarwar Shugaba Trump Ta Raba kan 'Yan Majalisar Amurka
Amurka - Sanarwar tsagaita wuta da kasar Musulunci ta Iran wadda Shugaba Donald Trump ya yi ta raba kawunan 'yan majalisar Amurka.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wasu daga cikin yan Majalisar Amurka sun yabawa matakin a matsayin mai kyau, yayin da wasu kuma ke kokwanton cancantar shugaban na jam'iyyar Republican na ci gaba da shugabanci.

Source: Getty Images
Jaridar Vangaurd ta tattaro cewa yan majalisar sun fadi ra'ayoyinsu ne jim kadan bayan Amurka/Isra'ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni biyu.
An nemi a tsige Shugaba Donald Trump
'Yar majalisar wakilai ta jam'iyyar Democrat, Alexandria Ocasio-Cortez, ta ce sanarwar tsagaita bude wutar da Trump ya yi "ba ta sauya komai ba."
Kamar yadda ta wallafa a shafinta na X, Ocasio-Cortez ta ce:
"Shugaba Trump ya yi barazanar kisan kiyashi ga al'ummar Iran, kuma har yanzu yana amfani da waccan barazanar."

Kara karanta wannan
Kasar Iran ta gano matsala a sharuddan tsagaita wuta, ta shirya koya wa Isra'ila darasi
Ta kara da cewa ayyukan Trump "sun riga sun tura kasar tamu zuwa matakin da ya kamata a tsige shi ko kuma a yi amfani da sashe na 25."
"Ko dai ta hannun majalisar ministocinsa ko kuma Majalisar Dokoki, dole ne a tsige shugaban daga mukaminsa," in ji ta.
Martanin Sanatar Amurka, Lindsey Graham
Sanata Lindsey Graham na jam'iyyar Republican, wanda aminin Trump ne kuma mai tsattsauran ra'ayi kan manufofin kasashen waje, ya ce akwai bukatar sanya idon majalisa domin "tantance gaskiyar tsagaita wuta da Iran."
"A wannan mataki na farko, ina taka-tsantsan matuka game da abin da yake gaskiya da abin da yake tatsuniya ko kuma jirkita bayani," in ji Graham.
Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Chuck Schumer, ya kira Trump da "mutumin da ba shi da lafiyar kwakwalwa kwata-kwata."
Ya fadi haka ne a matsayin martani ga barazanar da shugaban kasar ya yi cewa "gaba daya al'ummar Iran za ta mutu a daren nan."
Bayan tsagaita wuta, Schummer ya bayyana a shafinsa na X cewa:
"Na ji dadin yadda Trump ya janye kuma yake ta fafutukar neman hanyar fita daga barazanar da ya yi."
'Dan Majalisa ya yabawa Trump
Kevin Kramer, sanata daga jihar Dakota ta Arewa na jam'iyyar Republican, ya rubuta cewa yana godiya ga Trump saboda "sadaukarwar da yake yi ba tare da gajiyawa ba wajen kare Amurka
'Yar majalisar wakilai Yassamin Ansari daga Arizona ta bayyana cewa ta "samu natsuwa na dan lokaci" saboda tsagaita wutar.

Source: Getty Images
Amma ta nace cewa kalaman Trump "sun tabbatar da cewa ya fita daga hayyacinsa, kuma bai dace da mukamin shugabanci ko kowane matsayi na iko ba."
"Ko ta hanyar tsigewa ko ta amfani da sashe na 25, lokaci ya riga ya kure na a cire Donald Trump da Pete Hegseth daga kan mulki," in ji ta.
Dan majalisar wakilai na jam'iyyar Republican, Zach Nunn, ya rubuta a shafin X cewa "hankalinsa ya kwanta da wannan tsagaita wuta."
Trump ya taso kawayen kasar Iran
An ji cewa, Shugaba Donald Trump ya sanar da sanya harajin kashi 50 kan dukkan kayayyakin kowace ƙasa muddin aka kama ta da sayar wa Iran makamai.
A cewar Trump, za a sanya harajin ne kan dukkan kayayyakin da kasar ko kasashen da suke shigar da su Amurka, matakin da ya ce zai fara aiki nan take.
Shugaban ya gargaɗi abokan hulda da kawayen Iran cewa za su fuskanci hukunci mai tsanani muddin suka ci gaba da taimaka wa ƙasar Musuluncin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

