Ana Batun, Tsagaita Wuta, Isra’ila Ta Saba Ka’ida, Ta Hallaka Limamin Musulunci
- Majiyoyi sun bayyana cewa wani harin sama da Isra’ila ta kai a kudancin Lebanon ya yi sanadin mutuwar ‘yan mata uku daga gida daya
- Harin ya kuma haddasa mutuwar fitaccen limamin Lebanon, Sadiq al-Nabulsi, yayin da Hezbollah ta yi barazanar daukar fansa
- Rikicin kan iyakar kasashen biyu na ci gaba da tsananta, inda dubban mutane ke tserewa daga gidajensu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Beirut, Lebanon - Rahotanni daga hukumomin Lebanon da ma’aikatar lafiya sun tabbatar da cewa Isra'ila ta kai wani harin sama a kudancin kasar.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa harin ya yi sanadin mutuwar ‘yan mata uku kanana da kuma wani babban limamin Musulunci.

Source: Twitter
Isra'ila ta kashe limami a Lebanon
Rahoton Al Jazeera ya ce harin ya faru ne lokacin da aka kai hari kan wata mota da ke tafiya tsakanin kauyuka kusa da iyakar Isra’ila, inda aka buge ta kai tsaye ta kama da wuta.
An ce ‘yan matan daga gida daya suke, kuma suna tare da wasu ‘yan uwansu a lokacin da lamarin ya faru, yayin da wasu fararen hula suka jikkata.
Haka kuma, an ruwaito cewa harin ya kashe fitaccen limamin addini na Lebanon, Sadiq al-Nabulsi, kodayake ana sa ran karin bayani daga hukumomi.
Hukumomi da Hezbollah sun maida martani
Hukumomin Lebanon sun bayyana harin a matsayin wanda ya afkawa yankunan fararen hula, lamarin da ya jawo fushin jama’a da kira ga a dakatar da tashin hankalin.
Kungiyar Hezbollah ta yi alkawarin daukar fansa, tana mai cewa Isra’ila za ta “biya diyyar jinin” wadanda aka kashe, inda ta mayar da martani da harba rokoki zuwa yankunan Arewacin Isra’ila.
Wannan hari ya kara yawan fararen hula da ke rasa rayukansu a Kudancin Lebanon, inda hare-haren Isra’ila suka karu sakamakon farmakin da ake kai wa daga bangaren Hezbollah.
Hukumomin lafiya sun ce mutane da dama sun jikkata a hare-haren baya-bayan nan a yankuna kamar Habbush da kusa da Tyre, har ma da lalacewar wasu cibiyoyin lafiya.
Sojojin Isra’ila sun ce hare-harensu na nufin cibiyoyin kungiyar Hezbollah ne da mayakanta, tare da kira ga fararen hula su bar yankunan da ke cikin hadari, cewar MTV Lebanon.

Source: Facebook
Halin da ake ciki a kasar Lebanon
Rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Hezbollah na ci gaba da tsananta a kan iyakar kasashen, inda dubban mutane suka rasa matsugunansu a bangarorin biyu.
Kungiyoyin jin kai sun yi gargadi kan yiwuwar barkewar matsalar jin kai, tare da kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta binciki hare-haren da ke shafar fararen hula.
Iyalan wadanda abin ya shafa na cikin alhini, yayin da mazauna yankunan ke bayyana ‘yan matan a matsayin marasa laifi da suka fada cikin rikicin da ba su da hannu a ciki.
Yayin da tashin hankali ke ci gaba, mazauna Kudancin Lebanon na rayuwa cikin fargaba, inda da dama ke tserewa zuwa arewa domin tsira.
Trump ya jefi Najeriya da kikirar labaran bogi
Labari ya gabata a ranar Laraba cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana game da zargin yada labaran karya dangane da martanin Iran kan tsagaita wuta.
Trump ya bayyana cewa wani shafin yanar gizo daga Najeriya ne ya kirkiri labarin, yana mai zargin tashar CNN da yada bayanin da bai da makama ko wani tushe.
A ranar da aka tsagaita wutar yaki da Iran, Shugaban Amurka ya ce an umarci tashar da ta janye rahoton, yana gargadi game da yada labarai na karya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


