Bayan Tsagaita Wuta, Trump Ya Fadi Aikin da Amurka Za Ta Yi Tare da Iran

Bayan Tsagaita Wuta, Trump Ya Fadi Aikin da Amurka Za Ta Yi Tare da Iran

  • Shugaban Amurka, Mai girma Donald Trump, ya yi tsokaci kan tsagaita wutar da aka yi tsakanin kasarsa da Iran
  • Donald Trump ya bayyana cewa Amurka za ta yi aiki tare da Iran kan abin da ya shafi shirinta na nukiliya
  • Shugaban na Amurka ya kuma yi gargadin cewa ba za a bari Iran ta ci gaba da inganta sinadarin Uranium ba

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana aikin da kasarsa za ta yi tare da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa ba za a sake barin Iran ta inganta sinadarin Uranium ba.

Trump ya ce Amurka za ta yi aiki tare da Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Heather Diehl
Source: Getty Images

Shugaban na Amurka ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Laraba, 8 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Ana murna an tsagaita wuta, Trump ya yi maganar da za ta iya harzuka Iran

Wane aiki Amurka za ta yi da Iran?

Donald Trump ya kuma bayyana cewa ƙasashen biyu za su yi aiki tare don "haƙowa tare da kwashe" dukkan abubuwan nukiliya da ke karkashin kasa sakamakon hare-haren Amurka na shekarar da ta gabata.

"Amurka za ta yi aiki kafada da kafada da Iran, wadda muka tabbatar ta riga ta fuskanci abin da zai zama sauyin gwamnati mai albarka!"
"Ba za a sake inganta Uranium ba, kuma Amurka, tare da haɗin gwiwar Iran, za ta haƙo tare da kwashe dukkan 'kurar' Nukiliya da aka binne sosai (sakamakon hare-haren B-2 Bombers). Babu abin da aka taba tun daga ranar da aka kai harin."

- Donald Trump

Trump ya kuma bayyana cewa a matsayin ɓangare na tattaunawa da Tehran, "muna nan, kuma za mu ci gaba da tattaunawa kan janye haraji (Tariff) da takunkumai ga Iran."

An yi yarjejeniya tsakanin Amurka Iran

Wannan sanarwa ita ce sabon mataki da Trump ya ɗauka bayan ya janye barazanar kai hare-hare masu muni kan Iran, ƙasar da ya dade yana zargi da ƙoƙarin kera makaman nukiliya.

Kara karanta wannan

An samu kasa 1 da ta shawo kan Trump, Amurka za ta tsagaita wuta a yaki da Iran

Yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon mako biyu ta haɗa da sake buɗe Mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar man fetur kuma jigon yaƙin da aka kwashe kusan makonni shida ana yi.

Amurka ta kai hare-hare a Iran

Jaridar Vanguard ta ce a watan Yunin 2025, dakarun Amurka sun kai hari kan wuraren nukiliya guda uku a Iran, Fordo, Natanz, da Isfahan, ta amfani da manyan bama-bamai masu fasa ƙarƙashin ƙasa da aka harba daga jiragen yaƙi na B-2 stealth bombers.

A lokacin, Trump ya yi iƙirarin cewa samamen ya "kakkabe" ƙarfin nukiliyar Iran kuma ya mayar da shirin nata baya da shekaru da dama.

Sai dai, har yanzu ba a san takamaiman barnar da aka yi ba. Kafin hare-haren na bara, hukumar makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) ta ce Iran tana inganta uranium har zuwa kashi 60 cikin 100.

Amurka ta kai hare-hare a Iran
Jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Reza B
Source: Getty Images

Wannan mataki ya yi nisa fiye da matakin da ake buƙata don amfanin yau da kullum (na zaman lafiya), kuma yana kusa da kashi 90 cikin 100 da ake buƙata don kera makamin nukiliya.

Yayin da ƙasashen Yamma da Isra'ila suka daɗe suna zargin Iran da neman mallakar makaman nukiliya, Tehran ta sha musanta hakan.

Kara karanta wannan

Ana yakin Iran, Donald Trump ya yi magana kan Kim Jong Un

Iran ta kakkabo makamin Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar IRGC ta Iran sun samu nasara kan Amurka da Isra'ila.

Dakarun na IRGC sun samu nasarar kakkabo wani makami mai linzami na Amurka a sararin samaniyar Iran.

Hakazalika, dakarun sun kuma samu nasarar kakkabowa tare da lalata wasu jirage marasa matuka guda biyu na kasar Isra'ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng