Ba Boye Boye, An Ji Abin da Saudiyya da Wasu Kasashe Suka Yi yayin Sulhunta Amurka da Iran
- Firaministan Pakistan, Shahbaz Sharif ya bayyana kasashen da suka ba da goyon baya a kokarin sulhunta Amurka/Isra'ila da Iran
- Sharif ya mika godiya ga wadannan kasashe, wadanda suka kunshi Saudiyya, China, Turkiyya, Masar da kasashen Yankin Tekun Fasha (GCC)
- Wannan na zuwa ne bayan an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon makonni a yakin Amurka da Iran bayan fiye da wata guda
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Pakistan - Bayan shafe akalla kwanaki 40 ana musayar wuta, an samu nasarar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Kasar Pakistan ce ta jagoranci shirin sulhunta Amurka/Isra'ila da Iran, kuma duka kasashen sun amince da dakatar da kai wa juna hare-hare tun a daren jiya Talata.

Source: Getty Images
Pakistan ta gode wa Saudiyya da wasu kasashe
A wani rahoto da Al-Jazeera ta tattaro, Pakistan ta fito ta godewa duk kasashen da suka bada gudummuwa wajen dakatar da wannan yaki da ya jefa Gabas ta Tsakiya cikin tashin hankali.
Idan ba ku manta ba, Amurka da Iran sun tabbatar da cewa sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonnni biyu.
Firaministan Pakistan, Muhammad Shahbaz Sharif ya godewa kasashen China, Saudiyya, Turkiyya, Masar, da Qatar bisa goyon bayan da suka bayar ga tsarin tsagaita bude wuta.
Kasashen da suka taimaka aka tsagaita wuta
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa wadannan kasashe sun bayar da "gagarumin goyon baya mara iyaka wajen cimma matsayar tsagaita wuta" tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran.
Haka kuma, Sharif ya godewa kasashen Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa na Yankin Tekun Fasha (GCC).
Ya ce:
"Yayin da muke shirin fara tattaunawar Islamabad, ina mika godiyarmu ga China, masarautar Saudiyya, Turkiyya, Masar, da Qatar, bisa goyon baya mara iyaka da suka bada har aka tsagaita wuta, da kuma ba wa kokarin diflomasiyya dama domin neman kawo karshen wannan rikici baki daya."
"Ina kuma nuna matukar godiyata ga 'yan uwa kassshen Kungiyar Hadin Kan Larabawa na Yankin Tekun Fasha (GCC), wadanda goyon bayansu da jajircewarsu ga zaman lafiya a yankin ya kasance babban ginshiki ga kokarinmu.
"Shugabannin dukkan kasashen nan da kuma Amurka sun nuna hangen nesa na musamman, hikima, da kuma hakuri wajen ba wa zaman lafiya dama."

Source: Facebook
A karshe, Firaministan Pakistan ya godewa dukkan abokan hulda na fadin duniya wadanda suka tuntube su tare da nuna yabo ga kokarin da Pakistan ke yi domin samar da zaman lafiya.
Isra'ila ta amince da batun tsagaita wuta
A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Isra’ila sun bayyana cewa sun dakatar da kai hare-hare a yakin da suke yi da Iran, bisa yarjejeniyar tsagaita wuta.
A cewar dakarun sojin na Isra'ila, wannan shi ne matsayarsu bayan Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta na makonni biyu da Iran.
Sai dai rundunar ta kara da cewa a kasar Lebanon, dakarunta na ci gaba da kai hare-hare da kuma gudanar da ayyukan kasa kan kungiyar Hezbollah,
Asali: Legit.ng

