Isra’ila Ta Bayyana Matsayarta kan Sulhu da Iran, Ta Fadi Kasar da Za Ta Afkawa
- Sojojin Isra’ila sun sanar da matsayarsu game da kai hari a kan Iran bayan sanar da tsagaita wuta na tsawon makonni biyu
- Duk da tsagaita wutar, Isra’ila ta ce har yanzu tana ci gaba da kai hare-hare da ayyukan kasa a Lebanon kan kungiyar Hezbollah
- An bukaci dubban mazauna kudancin Beirut su fice daga gidajensu cikin gaggawa yayin da hare-haren ke ci gaba a yankin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa sun dakatar da bude wuta a yakin da suke yi da Iran, bisa yarjejeniyar tsagaita wuta.
Sojojin suka ce wannan shi ne matsayarsu bayan Shugaban Amurka ya sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta na makonni biyu da Iran.

Source: Getty Images
Sai dai rundunar ta kara da cewa a kasar Lebanon, dakarunta na ci gaba da kai hare-hare da kuma gudanar da ayyukan kasa kan kungiyar Hezbollah, cewar The Guardian.
Umarnin sojojin Isra'ila ga yan kasar Lebanon
A lokaci guda, sojojin Isra’ila sun umarci mazauna yankunan kudancin Beirut da su fice daga gidajensu, jim kadan bayan sanar da ci gaba da farmaki kan kungiyar.
Wannan ne karo na uku da rundunar ke bayar da irin wannan gargadi ga mazauna Lebanon tun bayan sanar da tsagaita wutar tsakanin Amurka da Iran.
Rundunar tsaron Isra’ila (IDF) ta bukaci mazauna unguwanni bakwai a Beirut da su bar gidajensu cikin gaggawa domin tsira da rayukansu musammna mata da yara da suke rayuwa a yankin.
Wannan umarni ya shafi manyan yankuna na birnin, inda tuni daruruwan dubban mutane suka rasa matsugunansu sakamakon irin wadannan gargadi da hare-hare da ake kaiwa.

Source: Facebook
Isra'ila za ta ci gaba da farmakar Lebanon
Mai magana da yawun rundunar ta harshen Larabci, Avichay Adraee, ya ce suna ci gaba da kai hari kan muhimman wuraren soja na kungiyar Hezbollah a kudancin Beirut.
Ya ce:
“Ba mu da niyyar cutar da ku, saboda haka, domin kare rayukanku, dole ne ku fice daga yankin nan take.”
Gwamnatin Isra’ila ta ce ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, amma ta jaddada cewa yarjejeniyar ba ta shafi Lebanon ba, sabanin wani bayani da Pakistan ta fitar.
Har yanzu kungiyar Hezbollah ba ta fito fili ta bayyana matsayarta kan wannan lamari ba, kamar yadda rahoton Al Jazeera ya ruwaito.
Martanin Iran kan yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka
Kun ji cewa Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya tabbatar da cewa dakarun ƙasar za su dakatar da duk wani harin kare-kai kan Amurka da Isra'ila.
Majalisar ƙolin tsaron ƙasa ta Iran ta bayyana yarjejeniyar a matsayin "nasara ga al'ummar Iran" tare da gargaɗin Amurka kan sake yin wani kuskure irin wannan da ta yi.
Iran ta yi iƙirarin cewa Amurka ta amince da haƙƙinta na tace sinadarin nukiliya a matsayin wani ɓangare na tattaunawar tsagaita wuta da za a yi da kasar Amurka.
Asali: Legit.ng
