Netanyahu Ya Fara Shiga Matsala a Isra'ila ana Cigaba da Yakar Iran da Makwabtan Kasashe

Netanyahu Ya Fara Shiga Matsala a Isra'ila ana Cigaba da Yakar Iran da Makwabtan Kasashe

  • Wani 'dan jam'iyyar adawa a Isra'ila, Yair Lapid ya zargi Firaministan kasarsa, Benjamin Netanyahu da gazawa ta fannin siyasa
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da Isra'ila ke ci gaba da take yarjeniyoyin da aka kulla wajen wanzar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya
  • Lapid ya gargadi cewa gyaran barnar siyasa da Netanyahu ya jawo wa kasarsa zai dauki tsawon shekaru kafin a samu gyara

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Israel - Jagoran ‘yan adawa a ƙasar Isra’ila, Yair Lapid, ya zargi Firaminista Benjamin Netanyahu da gazawa a bangaren siyasa bayan yarjejeniyar tsagaita wuta.

Lapid ya bayyana haka ne bayan Amurka da Iran sun cimma matsaya a kan tsagauta wuta na makonni biyu bayan yakin da aka fara tun a karshen watan Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da muka sani kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran

Ana ci gaba da sukar Netanyahu a cikin kasarsa
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: Benjamin Netanyahu
Source: Getty Images

A cikin sakon da Yair Lapid ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana takaici game da halin da Benjamin Netanyahu ya jefa Yahudawa.

An fara nuna damuwa kan Benjamin Netanyahu

Aljazeera ta wallafa cewa Yair Lapid ya kara da babu Isra'ila teburin sulhun da ake kokarin yanke muhimman bayanai game da yakin kasar.

Ya kara da cewa:

“Ba a taba samun irin wannan mummunar asarar siyasa ba a tarihinmu. Isra’ila ma ba ta zauna a teburin tattaunawa ba lokacin da ake yanke hukunci kan muhimman batutuwan tsaron ƙasa.”

Ya kara da cewa duk da kokarin da sojoji suka yi da kuma juriyar da al’umma suka nuna, gwamnatin Netanyahu ta gaza cimma burinta.

Ana zargin Netanyahu da tafka barna a Isra'ila
Benjamin Netanyahu yana jawabi a yayin wani taro a kasar Hoto: Benjamin Netanyahu
Source: Getty Images

Lapid ya ce:

“Sojoji sun aiwatar da duk abin da aka bukace su, jama’a sun nuna gagarumar juriya, amma Netanyahu ya gaza a siyasa, bai cimma ko daya daga cikin manufofin da ya kafa ba.”

Kara karanta wannan

An samu kasa 1 da ta shawo kan Trump, Amurka za ta tsagaita wuta a yaki da Iran

Za a dade ana gyara barnar Netanyahu

Ya kara da cewa sakamakon wannan gazawa, Isra’ila za ta shafe shekaru tana kokarin gyara barnar da aka yi a bangaren siyasa da dabarun tsaro.

A cewarsa, girman kai, sakaci da kuma rashin ingantaccen tsari su ne suka jefa kasar cikin wannan hali. Kalaman Lapid na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara a cikin gida kan yadda gwamnatin Netanyahu ta tafiyar da al’amuran tsaro da siyasa a wannan lokaci mai sarkakiya.

Haka kuma ana ci gaba da yaki da Iran, Lebanon da kuma kai haramtaccen hari a kan mutanen Gaza da ke neman zaman lafiya a cikin kasarsu ta Falasdinu.

Netanyahu ya soke yarjejeniya da hari kan Lebanon

A baya, mun wallafa cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi magana kan tsarin tsagaita wuta da Amurka da Isra'ila suka amince da shi.

A cikin sharuda 10 da Iran ta mika wa Shugaban Amurka, Donald Trump kuma ya amince da su akwai daina kai hari Lebanon wanda Isra'ila ke yi ba kakkautawa.

Sai dai a yanzu haka, Benjamin Netanyahu ya fito ya ce babu maganar daina kai hari Lebanon a cikin yarjejeniyar da aka yi, saboda haka ba zai fasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng