'Kowa Sai Ya Mutu': Trump Ya Fadi Lokacin da Zai Shafe Iran daga Doron duniya
- Shugaba Donald Trump ya gargaɗi Iran cewa zai shafe gaba daya kasar daga doron kasa a daren yau muddin ba ta buɗe mashigar Hormuz ba
- Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta riga sun fara kai hare-hare kan tsibirin Kharg, wanda shi ne babban wurin fitar da man fetur na kasar Iran
- Wannan shi ne karo na huɗu da Trump yake ɗaga wa'adin kai 'mummunan hari Iran,' inda a yanzu ya ce zai shafe kasar da ƙarfe 8:00 na dare
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka – Shugaba Donald Trump ya sake yin maganar da ta tayar da kura a yaƙin da Amurka take yi da kasar Iran a yau Talata, 7 ga watan Afrilu, 2026.
Shugaban kasar, ya lashi takobin cewa da misalin karfe 8:00 na dare, agogon ET, zai shafe Iran daga doron duniya muddin ba a cimma yarjejeniyar buɗe mashigin tekun Hormuz ba.

Source: Getty Images
Donald Trump na barazanar shafe kasar Iran
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya bayyana cewa:
"Za mu shafe gaba daya al'ummar kasar a yau, ba za a taba dawo da su ba. Ba wai ina son hakan ta faru ba ne, amma idan ta kama, to dole na aiwatar da hakan.
"Sai dai, yanzu da muka kammala canja gwamnatinsu, aka samar da sababbin shugabanni masu basira, masu karancin tsaurin ra'ayi, kila a samar da wata yarjejeniya mai ma'ana, komai zai iya faruwa.
"Amma dai yau ce ranar karshe, ranar da za ta shiga tarihin duniya, domin an dade ana jiran zuwan wannan ranar. Shekaru 47 na cin hanci da rashawa, kisan gilla, duk yau za su zo karshe. Ubangiji dai ya albashi al'ummar kasar Iran."
Wannan gargaɗi na Trump zuwa ne bayan da fadar White House ta tabbatar da cewa sojojin Amurka sun kai hari kan tsibirin Kharg, wanda shi ne matattarar man fetur na Iran.
Dalilin takun-saka kan mashigar Hormuz
Rikicin ya ta'allaka ne da toshe mashigar tekun Hormuz da Iran ta yi tun farkon yaƙin a watan Fabrairu, wanda hakan ya janyo tashin farashin man fetur a duniya.
Trump ya bugi kirji a lokacin cewa Amurka da Isra'ila sun riga sun ruguza dakarun sojin Iran, amma ya amince cewa har yanzu su ne ke da ikon juya zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar.
A ranar Lahadin Ista, Trump ya yi magana cikin kakkausar murya, har da dura ashariya, inda ya yi barazanar lalata gadaje da masana'antun wutar lantarki na Iran.
A ranar ne ya ya sanya ƙarfe 8:00 na daren yau Talata (8:00 p.m. ET) a matsayin lokacin da zai cika alkawarinsa na ragargazar manyan kadarorin Iran.

Source: Getty Images
Amai da lashewar da Trump ya yi kan Iran
Sai dai, rahoton BBC ya nuna cewa ba wannan ne karo na farko da Trump ke bayar da wa'adi ba; ya sha ɗaga lokacin kai harin tun daga ranar 21 ga Maris 2026 lokacin da ya ba da wa'adin sa'o'i 48.
Ya sake ɗaga wa'adin zuwa 28 ga Maris, sannan zuwa 6 ga Afrilu, kafin ya sanya wannan sabon wa'adi na daren yau Talata.
Gwamnatin Iran dai ta musanta cewa tana tattaunawa da gwamnatin Trump, kuma ta ci gaba da harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙA kan Isra'ila da ƙasashen Larabawa.
Yadda Trump ya tura bindigogi Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya bayyana yadda Amurka ta tura makamai lokacin da ake zanga-zanga a kasar Iran.
Trump ya bayyana cewa kasarsa ta aika makamai masu yawa domin tallafa wa masu zanga-zanga a Iran, amma ya yi zargin cewa Kurdawa sun kwashe su.
Kurdawa dai sun dade suna zaune a yankin arewacin Iraq kusa da iyakar Iran tun bayan juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979.
Asali: Legit.ng


