Shugaban Amurka, Trump Ya Cika Mamakin Abin da Ya Gani daga Mutanen Kasar Musulunci Ta Iran

Shugaban Amurka, Trump Ya Cika Mamakin Abin da Ya Gani daga Mutanen Kasar Musulunci Ta Iran

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayana tsantsar mamaki kan halin da mazauna kasar Iran ke nunawa duk da hare-haren da ake kai masu
  • Trump ya ce ya ga mutanen Iran na maraba da hare-haren da Amurka da Isra'ila ke kai wa duk da ana taba kusa da wuraren da suke rayuwa
  • Wannan na zuwa me bayan Amurka ta yi nasarar ceto matukin jirginta da ya makale a Iran bayan kakkabo jirgin da yake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Bayan shafe sama da wata guda ana musayar wuta, shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana abin da ya ba shi mamaki game da mutanen kasar Iran.

Shugaba Trump ya bayyana cewa yadda Iraniyawa ke rokon Amurka ta ci gaba da jefa masu bama-bamai a kusa da gidajen da suke zaune, ya yi matukar ba shi mamaki.

Kara karanta wannan

Ana yakin Iran, Donald Trump ya yi magana kan Kim Jong Un

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana jawabi ga yan kasa Hoto: Donald J. Trump
Source: Getty Images

BBC Hausa ta tattaro cewa a wani jawabi da ya gabatar, Trump ya ce abin mamaki ne yadda wasu daga cikin ‘yan Iran ke nuna kamar ba su damu da hare-haren ba.

Halin 'yan Iran ya ba Trump mamaki

Shugaban Amurka ya ce:

“‘Yan Iran da muka gani suna cewa ku ci gaba da jefa mana bam. Duk da cewa bama-bamai na fadawa kusa da gidajensu, suna ci gaba da cewa mu kara, abin mamaki ne matuka."

Trump ya kuma bayyana yadda ya bayar da umarni ga rundunar sojin Amurka da su yi duk abin da ya dace domin ceto wani matukin jirgin saman Amurka da ya shiga hadari a Iran.

A cewarsa, an gudanar da wani aiki na musamman cikin gaggawa wanda ya hada da tura jirage da dama cikin kasar Iran, kuma daga bisani an samu nasarar ceto matukin jirgin.

Ya bayyana wannan aiki a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan hadin gwiwar soji da aka gudanar cikin kankanin lokaci kuma aka samu nasara, kamar yadda NBC News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, Shugaban Amurka ya furta abin da yake kwadayin samu daga Iran

Barazanar Trump ga kasar Iran

Baya ga haka, Trump ya sake nanata matsayarsa kan Iran, inda ya yi barazanar cewa Amurka na da karfin da za ta iya rusa kasar gaba daya cikin kankanin lokaci idan har rikicin ya kara tsananta.

Ya ce:

“Za mu iya lalata dukkan Iran cikin dare guda, watakila ma a daren gobe.”
Mutanen Iran.
Mutanen kasar Iran yayin da suka fito zanga-zangar nuna goyon baya ga gwamnatin kasarsu Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Tasirin wannan furuci na Trump

Wannan furuci na Trump na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ke kara kamari, lamarin da ke haddasa fargaba a duniya baki daya.

Masana harkokin tsaro da siyasa na ganin irin wadannan kalamai na iya kara dagula al’amura, musamman idan aka yi la’akari da yadda rikicin ya riga ya shafi yankuna da dama a Gabas ta Tsakiya.

An kai wani mataki a sulhun Amurka da Iran

A wani labarin, kun ji cewa Jakadan Iran a Pakistan, Reza Amiri Moghadam ya yi bayani kan halin da ake ciki a kokarin kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Raina Musulunci: An zargi Trump da kira sunan Allah a yanayi maras kyau

Jakadan ya bayyana cewa kokarin da Pakistan ke yi don taimakawa wajen dakatar da yakin Amurka/Isra'ila da Iran ya kai wani mataki mai matukar muhimmanci da kuma sarkakiya.

Duk da bai bayyana lokacin da za a yanke shawara ta karshe ba, amma ya bukaci al'umma da su zama cikin shiri don jin sakamako nan gaba kadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262