Shugaban Iran da Mutum Miliyan 14 za Su Kare Wuraren da Trump zai Ruguza

Shugaban Iran da Mutum Miliyan 14 za Su Kare Wuraren da Trump zai Ruguza

  • Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce mutane miliyan 14 sun shirya sadaukar da rayukansu domin kare kadarorin kasar daga barazanar Donald Trump
  • Sanarwar da gwamnatin Iran ta fitar game da lamarin ta zo ne 'yan sa'o'i kadan kafin wa’adin da Amurka ta bayar kan bude mashigar ruwan Hormuz
  • A kan haka ne kasar Iran bukaci matasa su fito kwansu da kwarkwatar su domin kare muhimman cibiyoyin da Trump ya ce zai kai wa hari ranar Talata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa sama da mutane miliyan 14 a kasar sun amsa shirin sadaukar da rayukansu domin kare Tehran yayin da rikicinsu da Amurka ke kara kamari.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wa’adin da shugaban Amurka, Donald Trump ya bayar ke kara matsowa, inda ya yi barazanar kai hare-hare kan muhimman abubuwan more rayuwa a Iran.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, Shugaban Amurka ya furta abin da yake kwadayin samu daga Iran

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian
Masoud Pezeshkian yana magana da wasu shugabanni. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Miliyoyin mutane za su kare Iran

Masoud Pezeshkian ya bayyana a ranar Talata, 7 ga Afrilu, 2026, a wani sako da ya wallafa a X, cewa shi ma a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa tare da miliyoyin mutanen da za su kare kasar.

A cikin sakonsa, Pezeshkian ya ce:

“Fiye da mutane miliyan 14 a Iran sun bayyana shirinsu na sadaukar da rayukansu a wannan yunkuri. Ni ma na sadaukar da raina, kuma zan ci gaba da kasancewa a shirye na bayar da rayuwata domin Iran.”

Adadin ya ninka wasu alkaluman da kafafen yada labaran gwamnatin Iran suka taba ambata a baya, inda ake neman masu sa kai ta sakonnin waya da kafofin watsa labarai tun bayan fara yakin.

Al-Jazeera ta wallafa cewa Iran na da yawan jama’a kusan miliyan 90, kuma ana ganin wannan sanarwa na da nufin hana yiwuwar hare-haren da Amurka ke shirin kaiwa.

Kara karanta wannan

Raina Musulunci: An zargi Trump da kira sunan Allah a yanayi maras kyau

Shirin da mutanen kasar Iran ke yi

A gefe guda, hukumomin Iran sun bukaci matasa su gudanar da wani yunkuri na taruwa a kusa da manyan tashoshin lantarki a fadin kasar.

Ma’aikatar wasanni da matasa ta Iran ta yi kira ga matasa, ciki har da dalibai, ‘yan wasa da masu fasaha daban-daban, su taru a wuraren da aka ware da karfe 2:00 na rana a ranar Talata.

Wannan yunkuri na zuwa ne kusan sa’o’i 13 kafin wa’adin da Trump ya bayar na bude mashigin Hormuz ya kare, inda ya ce zai kai hare-hare.

Mataimakin ministan kula da harkokin matasa, Alireza Rahimi, ya ce wannan mataki shawara ce daga matasan da kansu domin nuna goyon baya ga kare muhimman abubuwan more rayuwa.

Isra'ila ta kai hari kan Yahudawa

A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin kasar Isra'ila ta kai wasu hare-hare da suka sauka a kan wajen bautar Yahudawa a Tehran.

Rahotanni sun tabbatar da cewa harin ya yi sanadiyyar lalacewar wajen da Yahudawa ke taruwa su yi bauta a babban birnin Iran.

Yayin da ake cigaba da tantance barnar da harin ya yi, Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu bai fito ya ce komai game da harin ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng