Dara Ta Ci Gida: Harin Isra'ila Ya Dura kan Yahudawa a Iran

Dara Ta Ci Gida: Harin Isra'ila Ya Dura kan Yahudawa a Iran

  • Bayan shafe sama da wata guda ana fafatawa, kasashen Iran da Amurka/Isra'ila na cigaba da kai hare-hare ga juna a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Wani mummunan hari da dakarun Isra'ila suka kai babban birnin Iran ya sauka kan wajen bautar Yahudawa, lamarin da ya jawo babbar barna
  • Hakan na zuwa ne yayin da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ke cigaba da tattauna batun daukar mataki kan bude mashigar Hormuz

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Kaikayi ya koma kan mashekiya a wani hari da sojojin Isra'ila suka kai Iran amma makaman suka sauka kan wajen bautar Yahudawa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka da Isra'ila ke cigaba da ruwan bama-bamai a Tehran, Iran kuma ke kai hare-hare zuwa Tel Aviv da wasu kasashe.

Kara karanta wannan

Babu sulhu da Iran, Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a garuruwa 12 na kasar Musulunci

Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu a wani waje da aka kai hari a Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Isra'ila ta kai hari kan Yahudawan Iran

Rahotanni daga kafar labaran Royal News sun ce hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra’ila da aka kai da safiyar Talata sun lalata wata majami’ar Yahudawa gaba daya a Tehran, babban birnin Iran.

Bayanan da aka samu sun nuna cewa:

“Bisa bayanan da aka tara da farko, majami’ar Rafi-Nia... ta lalace gaba daya a hare-haren da aka kai da safiyar yau,”

Addinin Yahudanci na daga cikin addinai da doka ta amince da su a Iran, kuma kasar na da al’ummar Yahudawa, duk da cewa da dama sun bar kasar bayan juyin juya halin 1979.

Babu cikakken kididdiga a hukumance da aka fitar, amma ana hasashen akwai dubban Yahudawa da ke zaune a Iran har yanzu.

Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu na magana a wajen taro a Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An bayyana majami’ar a matsayin daya daga cikin muhimman wuraren da Yahudawan Khorasan ke haduwa da gudanar da bukukuwa.

Ga bidiyon da Al-Jazeera ta wallafa a X kan harin:

Kara karanta wannan

Netanyahu ya yi magana da kasar Iran ta farmaki muhimmin wuri a Isra'ila

Shirin bude mashigar Hormuz

Bayan barazanar Rasha, China da Faransa kan kin amincewa da amfani da karfi, ana sa ran Kwamitin Tsaron majalisar dinkin duniya zai kada kuri’a kan mashigar Hormuz.

Sabon daftarin bai sake bada damar daukar matakin soja ba, ko da na kare kai, amma ya karfafi kasashe su hada kai wajen raka jiragen ruwa na kasuwanci.

Ana sa ran kada kuri’ar da karfe 11:00 na safe, sa’o’i kadan kafin wa’adin da Trump ya bayar kan cewa zai kai munanan hare-hare Iran.

Shugaban Amurka ya yi barazanar rushe gaba dayan gadar Iran da tashoshin lantarki cikin sa’o’i hudu idan ba a bude mashigar Hormuz ga zirga-zirgar jiragen ruwa na kasa da kasa ba.

Ana sa ran Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri’a a ranar Talata kan wani kuduri da ke kira a bude mashigar Hormuz.

An zargi Trump da raina Musulunci

A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban Amurka ya yi wasu maganganu da ake ganin akwai raina addinin Musulunci a ciki.

Kara karanta wannan

Bana ka taba: Faransa ta tura sojoji da tankokin yaki domin a yaki Isra'ila

Trump ya ambaci sunan Allah a wata sanarwa da ya fitar yayin yi wa kasar Iran barazanar kai manyan hare-hare kan rufe Hormuz.

Wata kungiyar addinin Musulunci a kasar Amurka ta bayyana cewa kalaman da Trump ya yi amfani da su sun nuna cin fuska ga Musulmi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng