Tirkashi: Trump Ya Fadi Lokacin da Dakarun Amurka Za Su Iya Kwace Iran

Tirkashi: Trump Ya Fadi Lokacin da Dakarun Amurka Za Su Iya Kwace Iran

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan lokacin da dakarun kasarsa za su iya kwace Iran
  • Donald Trump ya kuma bayyana cewa yakin da Amurka ke yi da Iran na tafiya yadda ya kamata, inda ya yaba kan ceto matukin jirgin yakin da aka yi
  • Shugaban na Amurka ya kuma tabo batun tattaunawar da ake yi domin ganin an kawo karshen yakin da ake yi

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan yakin da kasarsa ke yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Shugaba Donald Trump ya yi iƙirarin cewa yaƙin da Amurka ke yi da Iran yana tafiya yadda ya kamata.

Trump ya yi ikirari kan yakin Amurka da Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Andrew Caballero-Reynolds
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa Donald Trump, ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a ranar Litinin, 6 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, Shugaban Amurka ya furta abin da yake kwadayin samu daga Iran

Me Donald Trump ya ce kan kwace Iran?

Donald Trump ya kuma yi ikirarin cewa dakarun Amurka za su iya "kwace" daukacin ƙasar a cikin dare ɗaya rak.

“Ana iya kwace daukacin ƙasar a dare ɗaya. “Kuma wannan daren yana iya kasancewa daren gobe.”

- Donald Trump

Kalaman na Trump na nuni ne ga wa’adin da ya riga ya gindaya wa Iran na lallai ta buɗe Mashigar Hormuz a ranar Talata, 7 ga watan Afirilun 2026.

Trump ya tabo batun tattaunawa da Iran

Hakazalika, Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa Iran ta shiga cikin tattaunawar da ake yi domin kawo ƙarshen yaƙin "cikin son rai da ƙwazo."

“Ba zan iya magana kan tsagaita wuta ba, amma zan iya gaya muku cewa muna da sashe ɗaya (Iran) da ke son tattaunawa kuma yana bamu haɗin kai. Suna son su iya ƙulla yarjejeniya. Ba zan iya cewa uffan fiye da haka ba."

- Donald Trump

Tashar CNN ta ce Trump ya kuma shaida wa manema labarai cewa tattaunawar da ake yi ta hannun wasu ƙasashe don kawo ƙarshen rikicin tana "tafiya yadda ya kamata."

Kara karanta wannan

'Dan majalisar Amurka ya hango haɗarin cigaba da yaƙi da Iran

“A zahiri suna da lokaci har zuwa ƙarfe 8:00 na daren gobe (lokacin Amurka), amma muna tattaunawa da su. Ina jin abubuwa suna tafiya da kyau."
"Mista Witkoff yana nan kuma JD Vance yana cikin masu tattaunawar. Mista Witkoff yana zaune a nan kuma ina jin komai yana tafiya daidai, amma sai dai mu jira mu gani."

- Donald Trump

Trump ya ce ana tattaunawa da Iran
Shugaba Donald Trump na magana a gaban jirgin saman Amurka Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya yaba da ceto matukin jirgin Amurka

Haka zalika, shugaban na Amurka ya yaba da samamen da ya kai ga ceto matuƙan jirgin saman Amurka a Iran, inda ya bayyana shi a matsayin abin da ya kafa "tarihi."

“Na ba wa dakarun Amurka umarnin yin duk abin da ya dace don dawo da jarumanmu gida."

- Donald Trump

Trump ya kuma ƙara da cewa an yi amfani da jiragen yaƙin Amurka guda 21 yayin aikin ceton.

Iran ta sha alwashi kan Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sha sabon alwashi kan Amurka da Isra'ila.

Iran ta bayyana cewa duk wani kai hari kan wuraren farar hula zai fuskanci gagarumin martani mai tsanani daga dakarun tsaron ƙasar.

Kakakin hedkwatar tsaro ta Khatam al-Anbiya, Laftanar Kanar Ebrahim Zolfaqari ya bayyana cewa Iran za ta mayar da martani mai zafi idan aka ci gaba da farmakar wuraren fararen hula.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng