Magana Ta Fito, Shugaban Amurka Ya Furta Abin da Yake Kwadayin Samu daga Iran
- Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa zai so kwace danyen man kasar Iran idan ya samu damar hakan a yakin da Amurka ke yi da kasar
- Trump ya kafa misali da abin da ya yi wa Venezuela, inda ya ce Amurka na samun mai da yawa bayan kama tsohon shugaban kasar
- Alkaluman bincike sun nuna cewa yawancin Amurkawa ba sa goyon bayan matakin soji da Amurka ke dauka a Iran
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake bayyana kwadayinsa karara kan albarkatun man fetur na kasar Musulunci ta Iran.
Trump ya sanar da duniya cewa idan da za a ba shi zabi, zai so ya kwace danyen mai na kasar Iran gaba daya ya koma karkashin ikon kasar Amurka.

Source: Getty Images
Shugaban ya yi wannan furucin ne yayin da yake magana da manema labarai a taron Easter Egg Roll na fadar White House ranar Litinin, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta rahoto.
Abin da Trump ke son kwacewa a Iran
Trump ya bayyana cewa idan aka ba shi zabi, zai kwashe danyen man fetur din Iran, inda ya kara da cewa jama'ar Amurka ba sa son ganin sojojin Amurka sun ci gaba da yaki.
"Idan ina da zabi, me zan so in yi a Iran? Kwashe man fetur saboda yana nan a shirye tsaf, za a iya kwace shi. Babu abin da za su iya yi game da hakan.
"Abin takaici, al'ummar Amurka za su so su ga mun dawo gida. Idan da a hannuna abin yake, zan kwashe man, in rike shi, zan samu kudi masu yawa, sannan kuma zan kula da al'ummar Iran fiye da yadda aka kula da su a baya."
Trump ya tabo abin da ya yiwa Venezuela
Daga nan sai Trump ya yi nuni da danyen man fetur din da Amurka ke karba daga Venezuela bayan kama tsohon shugabanta, Nicolás Maduro, da matarsa a watan Janairu.

Kara karanta wannan
Iran ta fadi 'bazata' da za ta yi wa Amurka a yaƙi da Isra'ila bayan mata barazana
"Abubuwa sun tafi yadda ya kamata a Venezuela, a halin yanzu muna da gangar mai miliyan 100 a birnin Houston ana tace su. Wannan abu ne mai kyau sosai."

Source: Getty Images
Da aka tambaye shi ko wane sako yake da shi ga Amurkawa wadanda ba sa son yakin da ake yi da Iran, Trump ya ce:
"Wawaye ne, saboda yakin nan a kan abu daya ne: Iran ba za ta taba mallakar makamin nukiliya ba."
Rahoton NBC News ya nuna cewa alkaluman bincike sun nuna cewa yawancin Amurkawa ba sa goyon bayan matakin soji da Amurka ke dauka a Iran, amma 'yan jam'iyyar Republican sun ba wa matakan na Trump goyon baya.
Trump bai amince da batun tsagaita wuta ba
A wani labarin, kun ji cewa fadar shugaban kasar Amurka ta ce Shugaba Donald Trump bai amince da bukatar tsagaita wuta ta kwanaki 45 da aka gabatar ba.
Wani jami'i a fadar shugaban Amurka, a ranar Litinin, 6 ga Afrilu, 2026 ya ce ana ci gaba da nazari kan batun tsagaita wutar a halin yanzu.
Ya bayyana cewa Amurka na ci gaba da yaki da Iran karkashin shirin da ta sanyawa suna Operation Epic Fury har sai shugaban kasa ya umarci a dakata.
Asali: Legit.ng
