Ana Wata ga Wata: Trump Ya Dauki Matsaya bayan Iran Ta Yi Watsi da Tsagaita Wuta
- Fadar shugaban kasar Amurka ta ce Shugaba Donald Trump bai amince da bukatar tsagaita wuta ta kwanaki 45 da aka gabatar ba
- Wani jami'i a fadar White House ya bayyana cewa Amurka na ci gaba da yaki da Iran karkashin shirin da ta sanyawa suna Operation Epic Fury
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da musayar wuta a yakin Amurka, Isra'ila da Iran, wanda ya shafe fiye da wata daya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Washington, America - Rahotanni daga fadar shugaban kasar Amurka, White House sun nuna cewa har yanzu Shugaba Donald Trump bai aminta da sharuddan tsagaita wuta ba.
Sai dai Fadar White House ta tabbatar da cewa daftarin bukatar tsagaita wuta na kwanaki 45 a yakin da Amurka/Isra'ila ke ci gaba da yi da kasar Musulunci ta Iran, ya isa gaban Shugaba Trump.

Source: Getty Images
Amurka na nazari kan batun tsagaita wuta
A rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa, ta tattaro cewa wani jami'i a Fadar shugaban Amurka, a ranar Litinin, 6 ga Afrilu, 2026 ya ce ana ci gaba da nazari kan batun tsagaita wutar a halin yanzu.
A cewarsa, akwai yarjejeniya da ake dubawa ta tsagaita bude wuta na tsawon kwanaki 45 da Iran, sai dai Shugaba Donald Trump bai riga ya “sa hannu” a kan shawarar ba, kuma yana ci gaba da yakin.
Kafofin yada labarai na Amurka ciki har da NBC News sun ruwaito cewa Washington ta karbi shawarar da masu shiga tsakani suka gabatar na tsagaita bude wuta na kwanaki 45 a yakin Gabas ta Tsakiya.
Idan ba ku manta ba kasar Pakistan ta mika daftarin da ke kunshe da matakan da ake so kowane bangare ya dauka domin dakatar da wannan yaki da aka shafe kusan kwanaki 45 ana gwabzawa.

Kara karanta wannan
Pakistan ta tura sako ana cikin musayar wuta, ta gabatar da matakai 2 ga Amurka da Iran
Wace matsaya Trump ya dauka?
Wani jami'in fadar White House ya tabbatar da wannan yunkuri na Pakistan da sauran masu shiga tsakani, inda ya bayyana cewa:
“Wannan daya ne daga cikin dabarun da aka bullo da su (don ganin an kawo karshen yakin), amma POTUS (watau Shugaba Trump) bai sa hannu a kai ba.
"Ana nan ana ci gaba da fafatawa a karkashin shirin nan na Amurka mai taken 'Operation Epic Fury."

Source: Getty Images
Ya kara da cewa Shugaban Amurka zai yi karin bayani kan rikicin a wani taron manema labarai da aka shirya gudanarwa da karfe 1:00 na rana (17:00 agogon GMT).
Isra'ila ta kammala kai hari Tehran
A wani rahoton, kun ji cewa Isra’ila ta kai sabon hari a Tehran, babban birnin Iran, inda aka kashe aƙalla mutane 13 a ranar Litinin 6 ga watan Afrilu na shekarar 2026.
Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa sun kammala zagayen hare-hare kan wasu wuraren da suka kira na “gwamnatin Iran” a birnin Tehran.
Wannan hari na ranar Litinin ya biyo bayan gargadin da shugaban Amurka, Donald Trump , ya yi cewa dole Iran ta sake buɗe Strait of Hormuz.
Asali: Legit.ng
