Ba Boye Boye: Iran Ta Bayyana Matsayarta kan Tsagaita Wuta tsakaninta da Amurka

Ba Boye Boye: Iran Ta Bayyana Matsayarta kan Tsagaita Wuta tsakaninta da Amurka

  • Ana ta tattaunawa kan yiwuwar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran a yakin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya bayyana abin da Amurka ke son cimmawa kan batun tsagaita wuta
  • Esmaeil Baghaei ya bayyana cewa Amurka na son amfani da damar tsagaita wutar ne domin sake shirin ci gaba da yakin

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Kasar Jamhuriyar Musulunci Iran ta yi martani kan batun tsagaita wuta tsakaninta da Amurka.

Iran ta yi watsi da shawarwarin da Amurka ta gabatar na tsagaita wuta kan yakin da ake ci gaba da gwabzawa.

Iran ta yi martani kan bukatar Amurka
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da takwaransa na Amurka, Donald Trump Hoto: @drpezeshkian, @RealDonaldTrump
Source: Twitter

Tashar Press tv ta ce Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan

Pakistan ta tura sako ana cikin musayar wuta, ta gabatar da matakai 2 ga Amurka da Iran

Iran ta yi gargadin cewa duk wani dan takaitaccen lokaci da za a bayar sakamakon wannan tsagaita wuta, zai ba makiya damar sake shiri ne kawai domin aikata wasu karin laifuffuka kan al'ummar Iran.

Iran ta ki yarda da batun tsagaita wuta

Esmaeil Baghaei, ya yi bayani kan shawarwari daban-daban, ciki har da wata takarda mai dauke da abubuwa 15 daga Amurka kan yadda za a kawo karshen yakin.

Daga cikin abubuwan da shawarar ta kunsa, rahotanni sun nuna cewa Amurka na neman Iran ta daina ayyukanta na nukiliya na zaman lafiya, ta takaita shirinta na makamai masu linzami, sannan ta sake bude mashigar ruwa ta Hormuz wadda ta rufe wa makiya da kawayensu a matsayin ramuwar gayya.

Iran ta yi watsi da abubuwa biyun farko da ke cikin bukatar baki daya. Ta kuma jaddada cewa ba za ta amince da alkawuran "tsagaita wuta" na makiya wadanda suka shirya da kansu ba, ba tare da wani tabbaci ba.

Wadanne bukatu Iran ke nema?

Ta jaddada cewa tana neman kawo karshen kowane nau'in farmaki da ake kai wa kasar ne baki daya, tashar Anadolu Ajansi ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Ana sabon shirin kawo karshen yakin Iran, ana son tsagaita wuta na wasu kwanaki

Bugu da kari, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bukaci a biya ta diyya kan gagarumar barnar da maharan suka yi wa muhimman ababen more rayuwa na kasar daban-daban.

Baghaei ya kuma bayyana bukatun Amurka da ke cikin takardar a matsayin "wadanda suka wuce kima kuma ba a saba gani ba, sannan kuma marasa ma'ana."

Ya jaddada nacewar Iran kan bukatunata na halal, inda ya ce:

"Ba mu GT jin kunyar yin kururuwa kan bukatun halal da hakkokin al'ummarmu da na yankinmu."
Trump ya yi wa Iran barazana
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hotp: Heather Diehl
Source: Getty Images

Martanin Iran kan barazanar Trump

Kakakin ya yi nuni da barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na farmakar muhimman ababen more rayuwa na Iran idan har kasar ba ta amince da bukatun Washington na wuce kima ba.

Ya tabbatar da cewa Tehran za ta tsaya tsayin daka kan duk wani "wa'adi" na Amurka, yayin da yake nuna yadda ikirarin Washington na neman tattaunawar diplomasiyya ya saba wa ci gaba da aikata laifuka kan al'ummar Iran da kuma yi wa al'ummar barazana da karin laifukan yaki.

Sanatan Amurka ya magantu kan yaki da Iran

Kara karanta wannan

Amurka ta ji wuta, Trump ya nemi a tsagaita wuta a yakin da ake yi da Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Chris Murphy na jam'iyyar Democrat a Amurka, ya yi magana kan yakin kasarsa da Iran.

Sanata Chris Murphy ya bayyana cewa gwamnatin Trump ba ta da wani takamaiman tsari na tunkarar Iran, kuma tana shan kashi.

Chris Murphy ya bayyana cewa Amurka ba ta da wani babban tsari, wanda hakan ya sanya take yin rashin nasara a yakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng