Koriya Ta Arewa Ta Juya wa Iran baya, An Ji abin da Take Son Kulla wa da Amurka
- Hukumar leken asiri ta Koriya ta Kudu (NIS) ta bayyana cewa Kim Jong Un ya daina tura wa Iran makamai tun bayan ballewar yakinta da Amurka
- Hakazalika, Koriya ta Arewa ba ta aike da sakon ta'aziyya kan mutuwar jagoran Iran, Ayatollah Khamenei, ko taya dansa murnar karbar mulki ba
- NIS ta shaidawa majalisar kasar cewa Kim Jong Un na janye jikinsa daga Iran ne a wani yunkuri na kulla sabuwar alaka da Shugaba Donald Trump
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Koriya ta Kudu – Wani gagarumin sauyi na ban mamaki ya faru a siyasar duniya, inda rahotanni suka nuna cewa kasar Koriya ta Arewa ta fara zare jikinta daga kawarta ta tun-tuntuni, watau Iran.
Hukumar leken asiri ta Koriya ta Kudu (NIS) ta sanar da 'yan majalisar kasar cewa, Shugaba Kim Jong Un ya dauki wannan matakin ne domin kare damar kulla sabuwar alaka da gwamnatin Amurka idan an kammala yakin Iran.

Kara karanta wannan
Babbar Magana: Iran ta sha alwashi kan Amurka da Isra'ila ana shirin tsagaita wuta

Source: Getty Images
Koriya ta Arewa ta fara janye jiki da Iran
Kafar watsa labarai ta Reuters ta ruwaito wani dan majalisa, Park Sun-won ya na cewa:
"Koriya ta Arewa ba ta tura makamai ko kayayyakin yaki ga Iran ba tun farkon rikicin da ya barke a ranar 28 ga Fabrairu, 2026."
Abin da ya fi ba kowa mamaki shi ne yadda gwamnatin Kim ta yi gum da bakinta, a lokacin da Amurka da Iran suka kashe jagoran addinin Iran, Ayotallah Ali Khamenei, ko sakon ta'aziyya ba su aika ba.
Haka kuma, Koriya ta Arewa ba ta taya dansa, Mojtaba Khamenei, murnar zama sabon jagoran kasar Iran din ba. Wannan ya saba wa dabi'ar China da Rasha wadanda suka saba fitar da sanarwa akai-akai kan rikicin.
Ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ta fitar da sanarwa guda biyu kacal tun farkon yakin, wadanda aka tsara su cikin tausasa harshe domin kauce wa sukar Shugaba Trump kai-tsaye.
Dalilin Kim na kin shiga yakin Iran
Hukumar NIS ta bayyana cewa Kim Jong Un yana son samar da sararin tattaunawa ne kafin taron koli da ake sa ran za a yi tsakanin Shugaban China Xi Jinping da Donald Trump a watan Mayu, 2026, in ji rahoton The Japan Times.
A wani taron jam'iyyar su na karshen watan Fabrairu, Kim ya bayyana cewa:
"Ban ga dalilin da zai hana kasashenmu biyu su zauna lafiya ba muddin Amurka ta amince da matsayin mu na masu makaman nukiliya."
Wannan alama ce ta musamman da shugaban ya bayar domin nuna cewa yana son dinke barakar dake tsakanin Koriya ta Arewa da Amurka.

Source: Getty Images
Kalubalen tattalin arziki a Koriya Ta Arewa
Duk da wannan shiri na diflomasiyya, kasar Koriya ta Arewa na fuskantar matsin lamba a fannin tattalin arziki sakamakon yakin Iran.
An samu cikas wajen samar da kayayyakin masana'antu, hauhawar farashin kayayyaki, da kuma karyewar darajar kudinsu.

Kara karanta wannan
Iran ta fadi 'bazata' da za ta yi wa Amurka a yaƙi da Isra'ila bayan mata barazana
A halin yanzu, Koriya ta Arewa na kokarin neman man fetur daga kasar Rasha domin farfado da tattalin arzikinta, in ji rahoton The Jerusalem Post.
Hukumar NIS ta tabbatar wa 'yan majalisa cewa wannan kokari na Kim Jong Un na nuna cewa yana son raba kansa da duk wani abu da zai bata wa Trump rai, domin samun saukin takunkumin tattalin arziki dake addabar kasarsa.
Koriya ta harba makami tekun Japan
A wani labari, mun ruwaito cewa, Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami tekun Japan, kwanaki bayan ta yi gargadi kan atisayen sojan hadin gwiwa tsakanin Amurka.
Harin ya zo ne yayin da ake rade-radin yiwuwar haduwar shugabannin Amurka da Koriya ta Arewa a China, lamarin da zai iya sake bude kofar tattaunawa.
Sai dai gwamnatin Kim Jong Un ta soki kokarin zaman lafiya na baya-bayan nan, tana mai cewa ba za ta canza matsaya kan mallakar makaman nukiliya ba.
Asali: Legit.ng
