Babu Sulhu da Iran, Amurka da Isra'ila Sun Yi Babbar Barna a Garuruwa 12 na Kasar Musulunci

Babu Sulhu da Iran, Amurka da Isra'ila Sun Yi Babbar Barna a Garuruwa 12 na Kasar Musulunci

  • Hare-haren sama na hadin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a birnin Tehran da wasu garuruwan Iran
  • Tun bayan ballewar wannan yaki, mutane fiye da 1,900 ne aka tabbatar sun mutu a kasar Iran kadai, adadin da zai iya karuwa a wannan mako
  • Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marar matuka kan birnin Haifa na Isra'ila da kuma kasashen tekun Fasha

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran – Mutane sun shiga tsananin firgici a Iran bayan da dakarun Amurka da na Isra’ila suka kaddamar da jerin hare-hare ta sama kan manyan biranen kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa an ji karar tashin bama-bamai da kukan jiragen yaki na sa'o'i da dama a sararin samaniyar birnin Tehran yau.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Isra'ila da Iran ta harba miyagun makamai 10 lokaci 1

Amurka da Isra'ila sun kaddamar da hare-hare kan garuruwan Iran
An hango hayaki mai kauri ya tashi a birnin Tehran bayan harin Amurka da Isra'ila. Hoto: Tolga Akbaba/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

Amurka, Isra'ila sun kai hari Iran

Daya daga cikin hare-haren ya shafi shahararriyar jami'ar fasaha ta Sharif (SUT), sannan an ga bakin hayaki na tashi kusa da dandalin Azadi Square, in ji rahoton Aljazeera.

Ko da yake babu dalibai a cikin jami'ar saboda an koma karatu ta intanet, amma harin ya lalata gine-gine da wani babban wurin rarraba iskar gas dake kusa da harabar makarantar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa akalla mutane 13 ne suka riga mu gidan gaskiya a wani harin da aka kai kusa da Eslamshar, dake kudu maso yammacin Tehran.

Sauran wuraren da abin ya shafa sun hada da Birnin Qom, inda mutum biyar suka mutu, sannan mutane tara suka mutu a wasu sassa daban daban na Tehran

Jerin garuruwan da Amurka ta farmaka a Iran

Hakazalika, rahoton jaridar The Hill ya nuna cewa hare-haren da Amurka da Iran suka shafe awanni suna kai wa a Iran sun shafi garuruwan Bandar Abbas, Ahvaz, inda aka farmaki filin jirgin sama.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta yi kurman baƙi, ta ce ta kammala kai hare hare zuwa Iran

Bugu da kari, hare haren sun shafi birnin Mahshahr da Bandar-e Lengeh, Shiraz, Isfahan, Karaj, Qom, inda mutane biyar suka mutu, sannan an kashe mutane shida a Kong City, yayin da 17 suka jikkata.

Tun bayan ballewar wannan yaki, mutane fiye da 1,900 ne aka tabbatar sun mutu a kasar Iran kadai, kodayake gwamnatin kasar ba ta sabunta adadin wadanda suka mutu ba tsawon kwanaki.

Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hare hare kan Isra'ila da kasashen Gulf.
Wani makami mai linzami da Iran ta harba zuwa cikin Tel Aviv na Isra'ila. Hoto: Mostafa Alkharouf/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

Martanin hare-hare daga kasar Iran

A matsayin martani, Iran ta harba makaman linzami kan birnin Haifa dake arewacin Isra'ila, inda aka gano gawarwakin mutane biyu a karkashin baraguzan wani gini.

Haka kuma, Iran ta matsa wa makwabtan ta na yankin tekun Fasha lamba, inda kasashen Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), da Saudiyya suka kunna na'urorin kariyarsu domin kakkabo makaman linzami da jirage marar matuka da Iran ke harba wa.

Iran ta harba makamai 10 kan Isra'ila

A safiyar Litinin, Legit Hausa ta ruwaito cewa, Iran ta harba makamai masu linzami fiye da 10 a lokaci guda, a wani jerin hare-hare uku da suka firgita tsakiyar ƙasar Isra'ila.

Yayin da mutane ke hudun ceton rai bayan an kunna kararrawar gargadi, an rahoto cewa wata dattijuwa ta ji mummunan rauni a Tel Aviv.

Rahotanni sun nuna cewa Iran ta yi amfani da sababbin makamai masu tarwatsewa tun suna a sama domin rikita shingen tsaron Isra'ila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com