Raina Musulunci: An Zargi Trump da Kiran Sunan Allah a Yanayi Maras Kyau
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi wasu kalamai da suka shafi addinin Musulunci a ranar Lahadi, lamarin da ya ja hankalin duniya
- Trump ya yi maganar ne game da wani samame da ya sa aka yi a kasar Iran domin ceto sojan Amurka da ya makale bayan harbo jirginsa
- Shugaban yana shan suka game da furucin da ya yi, inda wasu kungiyoyi ke cewa akwai alamar raina addinin Musulunci a maganarsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaba Donald Trump da wasu jami’an gwamnatin Amurka sun bayyana ceto wani matukin jirgin sama na Amurka a Iran a matsayin 'mu’ujizar Easter' a ranar Lahadi.
Rahotanni sun nuna cewa sun gabatar da lamarin da salo na addini, suna nuna yakin a matsayin abin da ya dace kuma mai cike da albarkar Ubangiji.

Source: Getty Images
Rahoton Reuters ya nuna cewa kungiyar Council on American-Islamic Relations ta yi korafi game da amfani da lafuzan da suka shafi addini da Trump ya yi.
Donald Trump ya kira sunan Allah
A wani sako da ya yi amfani da addini, Trump ya yi barazana a shafukan sada zumunta cewa zai kai hari kan tashoshin lantarki da gada a Iran.
Trump ya kuma bukaci Tehran ta bude mashigar Hormuz, yana cewa “ku mahaukata” ko kuma su fuskanci rayuwa cikin bala'i, sannan ya kammala sakon da kalmar:
“Dukkan yabo sun tabbata ga Allah.”
An zargi Trump da raina Musulunci
Anadolu Agancy ta wallafa cewa kungiyar Council on American-Islamic Relations ta yi Allah-wadai da kalaman Trump, tana cewa a cikin wata sanarwa:
“Yin ba’a ga Musulunci da kuma barazanar kai hari kan abubuwan more rayuwa na fararen hula abu ne mai hatsari da rashin hankali."
Kungiyar ta ce amfani da lafazin da ya shafi Musulunci a yanayin barazanar tashin hankali na nuna yadda ake amfani da addini a matsayin makami tare da nuna rashin girmamawa ga Musulmi da akidunsu.
Kokarin kore alakar yakin da addini
A watan da ya gabata, wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka 30 daga jam’iyyar Democrat sun bukaci Sufeto Janar na Ma’aikatar Tsaro, Platte Moring, da ya yi bincike kan amfani da addini a yakin.
An bukaci ya binciki rahotannin da ke cewa wasu a cikin rundunar sojin Amurka sun yi kokarin kare yakin Iran ta hanyar amfani da wasu bayanai na addinin Kirista.
“A lokacin da biliyoyin daloli da rayuka masu yawa ke cikin hadari yayin da gwamnatin Trump ke gudanar da yakin da ta zaba a Iran, yana da matukar muhimmanci a raba addini da gwamnati da kuma kare ‘yancin addini na sojojinmu,”
Inji wasikar da aka aike wa sufeto janar din

Source: Getty Images
Batun tsagaita wuta a yakin Iran
A wani labarin, mun kawo muku cewa masu shiga tsakani daga wasu kasashe sun fara magana kan yadda za a kawo karshen yakin Iran da Amurka/Isra'ila.
Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa an tura bukatar tsagaita wuta ta kwana 45 ga kasashen Iran da Amurka bayan wata tattaunawa.
Masu shiga tsakanin sun bayyana cewa ana fatan a samo hanyar tsayar da yakin gaba daya idan aka cimma yarjejeniyar a matakin farko.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

