Dan Arewacin Najeriya da Ya Zama Sojan Amurka Ya Yi Magana kan Yakin Iran
- Wani dan Najeriya daga jihar Kano da ya zama sojan Amurka, Suleiman Isah Isah ya yi magana kan yakin da ake da Iran a Gabas ta Tsakiya
- Hakan na zuwa ne bayan lalata wasu jiragen Amurka masu darajar Dala miliyan 100 da aka yi a Iran yayin aikin ceto wani sojan kasar
- 'Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu game da maganar Suleiman Isah Isah a kan yadda Amurka ke kokarin ceto rayuwar dakarunta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Jiragen sama da Amurka ta yi amfani da su yayin wani aikin ceto a Iran, sannan daga baya aka lalata su, kowannensu ya kai darajar sama da Dala miliyan 100.
An yi amfani da jiragen MC-130J ne a wani aikin ceto ma’aikatan jirgin yaƙi na F-15E da suka faɗi a wani yunkurin kai hari ta sama a Iran.

Source: Facebook
Dan jihar Kano da ya shiga rundunar sojin Amurka, Suleiman Isah Isah ya wallafa sako a shafinsa na Facebook game da aikin ceton da aka yi.
Jirgin Amurka da aka lalata
Rahoton da tashar TRT ta wallafa cewa Amurka ta kera jirgin MC-130J domin saukar da sojoji da fitar da su daga wuraren da ke da haɗari.
Haka kuma, jirgin na ɗauke da na’urorin kariya na zamani, ciki har da na’urorin gano haɗari da ke taimakawa wajen kauce wa barazanar kariyar sararin samaniya kamar makamai masu linzami.
Wani jami’in gwamnatin Amurka ya ce an lalata jiragen MC-130J guda biyu yayin aikin ceto a Iran, ba tare da bayyana yadda aka rasa su ba.
Martanin sojan Amurka dan Najeriya
Dan jihar Kano da ya shiga soja a Amurka, Suleiman Isah Isah ya koka kan yadda 'yan Najeriya ke ta magana kan asarar jiragen da aka yi wajen ceto soja a Iran.
Suleiman ya ce:
“Mutane na farin ciki da asarar jiragen Amurka na dala miliyan 100 amma ba sa gane cewa Amurka na daraja rayuwar sojinta fiye da kuɗin waɗannan jirage. Ba a Najeriya ba ne aka kama wani Manjo Janar amma gwamnati ta kasa cetonsa?”
“...Muna daraja dukiya fiye da rayuwar sojojinmu a Najeriya.”
Yakin Iran: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya
'Yan Najeriya da dama sun yi wa sojan martani, wasu na masa tambayoyi, wasu kuma na nuna cewa gwamnatin tarayyar kasar ma na kokari.
Yazid Salisu ya ce:
“Malam sun lalata jiragen ne domin hana satar fasaha.”
AbdulAziz Adamu Maina ya ce:
“Ƙoƙarin da Amurka ta yi a aikin ceton ya kayatar matuƙa. Wannan na nuna yadda suke daraja rayuwar sojojinsu. Ina fatan ƙasata za ta kwaikwayi hakan.”
Habeeb Jikan Liman ya ce:
“Har ma ƙasashe masu ƙarfi kamar Amurka sun taɓa kasa ceton jami’ansu. Haka kuma Najeriya ma ta yi ƙoƙari a lokuta masu wahala. Ba ko yaushe ba ne a ke kallon lamarin tsakanin kuɗi da ceto rayuwa.”
Abdullahi Suleiman ya ce:
“Amurka ma ta gaza a wasu ayyukan ceto musamman a Afghanistan.”

Source: Facebook
Aminu Muhammad Bawa ya yi tambaya da cewa:
“Suleiman Isah Isah, mene ne ra’ayinka kan matakan da Trump ke ɗauka a Gabas ta Tsakiya? Daidai ne ko kuskure?”
Sani Bala Jalingo ya ce:
“Ina fatan dai ba za a tura ka Iran ba? Saboda muna sonka kuma muna son Iran. Idan aka ce za ku je ku kwace mashigar Hormuz, ka tuna da fim ɗin Ibro Soja a farkon Boko Haram.”
An kori dan Amurka a Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya ce an kori Alex Barbie daga Najeriya.
Alex Barbie wani dan Amurka ne da ya shigo wasu jihohin Arewa da sunan taimakon Kiristoci amma aka ga yana kira da a dauki makami.
Barbie ya sanar da cewa ya fita daga Najeriya, inda ya yi magana kan Dr Ahmad Gumi amma Bashir Ahmad ya ce umartansa aka yi ya bar kasar.
Asali: Legit.ng


