Isra'ila Ta Yi Kurman Baƙi, Ta Ce Ta Kammala Kai Hare Hare zuwa ran
- Isra’ila ta kai sabon hari a Tehran, inda aka kashe aƙalla mutane 13 a ranar Litinin 6 ga watan Afrilu na shekarar 2027
- Iran ta yi barazanar ramuwar gayya mai tsanani, da kowa zai ji ba dadi idan aka ci gaba da kai hari kan fararen hula
- Isra'ila ta yi magana inda ta ce ta 'kammala' kai wa Tehran hare-haren da ita da Amurka suka fara a ƙarshen Fabrairu, 2026
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Israel– Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa sun kammala zagayen hare-hare kan wasu wuraren da suka kira na “gwamnatin Iran” a birnin Tehran.
Rahotanni sun ce akalla mutane 13 ne suka mutu sakamakon harin da aka kai a safiyar ranar Litinin 6 a watan Afrilu, 2026.

Source: Facebook
Al-Jazeera ta wallafa cewa wannan na zuwa ne bayan harin da ya kashe mutum 13 a Gabashin Tehran da wasu mutum hudu a Baharestan County.
Isra'ila ta kara kai hari Iran
The Hindu ta wallafa cewa hare-haren sama da aka kai da sassafe sun kuma shafi jami'ar fasaha ta Sharif, daya daga cikin manyan jami’o’i a Iran.
Sai dai jim kadan bayan harin sojojin iska bayyana cewa sun kammala kai hare-hare kan gwamnatin Tehran a yanzu, amma ba su yi ƙarin bayani kan abin da hakan ke nufi ba.

Source: Twitter
Wannan hari na ranar Litinin ya biyo bayan gargadin da tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi cewa dole Iran ta sake buɗe Strait of Hormuz.
A bangaren Iran kuwa, rundunar sojin kasar ta yi gargadin cewa za ta dauki matakin ramuwar gayya mai matukar tsanani idan aka kai hari kan fararen hula.
Kasar Iran ta sake aika gargaɗi
Ministan al’adu na Iran, Sayed Reza Salihi-Amiri, ya yi watsi da barazanar Trump, yana mai kiran sa da mutum marar kan gado kuma ruɗaɗɗe.
Ya kara da cewa mashigar Hormuz a bude take ga duniya, amma a rufe take ga makiyan Iran, wanda ke nufin Amurka, Isra'ila da abokan hulɗarsu.
Rahotanni sun nuna cewa Iran ta kai hare-hare kan wasu muhimman kayayyakin more rayuwa a kasashen makwabta na yankin Gulf, lamarin da ya kawo cikas ga Amurka kan ceto wani jami’in sojinta da aka ɓaro.
Haka kuma, Iran ta yi barazanar takaita zirga-zirga a wata muhimmiyar mashigar ruwa ta yankin, wato Bab el-Mandeb, wacce ake amfani da ita sosai wajen jigilar kaya da mai.
Iran ta yi wa Isra'ila illa
A baya, mun wallafa cewa lasar Iran ta bayyana irin illar da ta yi wa Isra'ila yayin ta ke ci gaba da hana wasu kasashe bi ta hanyar mashigar ruwan Hormuz.
Rundunar 'Islamic Revolutionary Guards Corps' da ake kira IRGC ta dauki alhakin kai hari kan wani jirgin ruwan Isra'ila da ya yi kunnen ƙashi zai wuce ta Hormuz.
Tashin hankalin yankin ya kara tsananta sakamakon rikicin Iran da Amurka da Isra’ila wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi, kuma har yanzu ana musayar wuta.
Asali: Legit.ng

