Iran Ta Yi Wa Isra’ila Babbar Illa a Mashigar Hormuz bayan Babbake Jirgin Ruwanta
- Kasar Iran ta bayyana irin illar da ta yi wa Isra'ila yayin ta ke ci gaba da hana wasu kasashe bi ta hanyar mashigar ruwan Hormuz
- Rundunar 'Islamic Revolutionary Guards Corps' da ake kira IRGC ta dauki alhakin kai hari kan wani jirgin ruwan Isra'ila
- Tashin hankalin yankin ya kara tsananta sakamakon rikicin Iran da Amurka da Isra’ila wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Kasar Iran ta bayyana cewa wani jirgin ruwa mai alaka da Isra’ila ya kama da wuta bayan an kai masa hari.
Majiyoyi suka ce rundunar IRGC ta kasar Iran ta kai harin ne da jirgin mara matuki a mashigar Hormuz da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Rahoton Anadole Ajansi ya ce rundunar 'Islamic Revolutionary Guards Corps' ta sanar da cewa ta dauki alhakin kai wannan hari a ranar Asabar 4 ga watan Afrilun 2026.
Rundunar IRGC ta illata Amurka da Isra'ila
Rundunar tsaro ta IRGC da ke kasar Iran ta bayyana nasarar da ta samu yayin da ake ci gaba da yaki a Gabas ta Tsakiya.
IRGC ta ce ta lalata bama-bamai 120 a yankin Fars wadanda aka jefa yayin hare-haren Amurka da Isra’ila kwanaki da suka gabata.
Rahoto ya ce an gano su a kauyen Kafri da wasu yankuna da ke kusa dauke da bama-baman wadanda ke da mugun hatsari.

Source: Facebook
IRGC ta babbake jirgn ruwan Isra'ila
Sanarwar ta fito ne ta hannun rundunar ruwan IRGC, inda ta ce jirgin mai suna MSC Ishika ya kama da wuta sosai bayan harin.
Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa daga bangaren Isra’ila da ke tabbatar ko musanta ikirarin Iran.
Rikicin yankin Gabas ta Tsakiya ya kara tsananta tun bayan harin hadin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026.
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun yi sanadin mutuwar sama da mutane 1,340, ciki har da jagoran addini na Iran na wancan lokaci.
A martanin da Iran ke mayarwa, ta rika kai hare-hare da makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan Isra’ila da wasu kasashe makwabta.
Kasashen da abin ya shafa sun hada da Jordan, Iraq da kuma wasu kasashen yankin Gulf da ke dauke da sansanonin sojin Amurka, cewar rahoton Reuters.
Haka kuma Iran ta takaita zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, wadda ke da muhimmanci ga harkokin kasuwancin man fetur a duniya.
Iran ta farmaki muhimman wurare a Isra'ila
A baya, an ji cewa yakin da ake gwabzawa tsakanin kasashen Amurka, Isra'ila da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya na kara daukar zafi.
Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta kaddamar da hare-hare masu zafi kan Amurka da Isra'ila.
IRGC ta bayyana cewa ta farmaki muhimman wurare hare-haren da ta kai, inda ta nuna cewa ga cikin akwai wuraren ajiye jirage marasa matuka.
Asali: Legit.ng

