Magana Ta Fito: Yadda Trump Ya Tura Bindigogi Iran don a Yaki Gwamnatin Musulunci
- Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ta aika makamai da dama domin taimaka wa masu zanga-zanga a Iran
- Ya kuma yi barazanar kai hare-hare kan cibiyoyin wutar lantarki idan Iran ba ta bude mashigar Hormuz ba
- Rahotanni sun nuna rikicin ya kara tsananta yayin da farashin mai ke tashi, duk da cewa Amurka na ikirarin ta kusa samun nasara a yakin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana yadda Amurka ta tura makamai lokacin da ake zanga-zanga a kasar Iran.
Trump ya bayyana cewa kasarsa ta aika makamai masu yawa domin tallafa wa masu zanga-zanga a Iran, amma ya yi zargin cewa Kurdawa sun kwashe su.

Source: Getty Images
Trump ya magantu kan zanga-zanga a Iran
A wata hira da yan jarida, Trump ya nuna cewa Amurka ta shiga kokarin tayar da rikici a Iran tun kafin fara hare-haren soji, cewar Times of India.

Kara karanta wannan
Iran ta fadi 'bazata' da za ta yi wa Amurka a yaƙi da Isra'ila bayan mata barazana
Ya fara ranar Easter da kalamai masu tsauri, inda ya yi barazanar kai hari kan Iran idan ba a bude mashigar ruwa ta Hormuz ba cikin gaggawa.
Zanga-zangar da ta barke a farkon shekara ta jawo matsin lamba ga gwamnati, amma daga karshe an murkushe ta da karfi.
Trump ya ce an aika makamai ta hannun Kurdawa, amma ya yi zargin cewa su ne suka rike makaman maimakon kai su ga masu zanga-zanga.
Kurdawa dai sun dade suna zaune a yankin arewacin Iraq kusa da iyakar Iran tun bayan juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979.

Source: Getty Images
Barazanar Trump ga kasar Iran
A cewarsa, jami’an Iran sun kashe sama da mutane dubu arba’in yayin da suke murkushe zanga-zangar da ta dauki makonni ana yi, cewar Independent.
Shugaban ya kuma yi barazanar cewa zai kai hare-hare kan muhimman cibiyoyin more rayuwa idan ba a cimma yarjejeniya da Iran ba.
Masana sun ce irin wannan hari kan kayayyakin fararen hula na iya zama laifin yaki idan ba su da alaka da harkokin soja.
Trump ya kara da cewa babu abin da ba zai yi ba idan tattaunawa ta gaza, yana mai cewa za su iya lalata kasar baki daya.
A wani bangare, ya bayyana yadda aka ceto wani sojan Amurka bayan jirginsa ya fadi a Iran, inda aka yi tsawon lokaci ana nemansa.
Ya yi amfani da kalamai masu tsauri wajen bayyana mutanen Iran, lamarin da wasu ke ganin yana dauke da wariyar launin fata.
An musanta rashin lafiyar Trump
An ji cewa Fadar White House na Amurka ta yi karin haske kan rade-radin cewa Donald Trump yana asibitin Walter Reed domin samun kulawa.
Jita-jitar ta biyo bayan sanarwar cewa shugaban ba zai fito bainar jama’a ba a ranar wanda ya tayar da maganganu a tsakanin mutane.
Trump ya kuma yi gargadi ga kasar Iran da ba ta wa’adin awa 48 kan yarjejeniya ko daukar matakin soja a yakin da ake yi.
Asali: Legit.ng
