Iran Ta Nuna wa Trump Yatsa, Ta Lalata Hatsabiban Jirage da Amurka Ke Ji da Su

Iran Ta Nuna wa Trump Yatsa, Ta Lalata Hatsabiban Jirage da Amurka Ke Ji da Su

  • Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun sanar da kakkabo wani jirgin yaƙin Amurka samfurin MQ-9 Reaper a birnin Isfahan
  • Iran ta kuma yi da’awar lalata wani babban jirgin leƙen asirin Amurka samfurin E-3 Sentry a wani hari da ta kai sansanin sojojin Saudiyya
  • Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta yi asarar aƙalla jiragen yaƙi 16 tun farkon wannan rikici, ciki har da waɗanda hatsari ko kuskure ya rutsa da su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran – Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun yi nasarar kakkabo wani jirgin yaƙin Amurka maras matuƙi samfurin MQ-9 Reaper a sararin samaniyar birnin Isfahan dake tsakiyar ƙasar.

A cikin wata sanarwa da suka fitar, rundunar ta IRGC ta bayyana cewa na'urorin kariyarsu na zamani ne suka gano jirgin tare da ruguza shi baki ɗaya a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Yadda Iran ta riƙa kakkaɓo jiragen 'maƙiya' daga sararin samaniyarta

Iran ta kakkabo wasu hatsabiban jiragen yakin Amurka.
Jirgin yaki marar matuki na Amurka samfurin MQ-9 Reaper. Hoto: Miguel J. Rodriguez Carrillo / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta lalata hatsabiban jiragen Amurka

Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun fitar da bidiyon da ke nuna lokacin da makami ya daki jiragen MQ-9 guda biyu, lamarin da ya haifar da gagarumin fashewa a sararin samaniya, in ji rahoton Aljazeera.

Wannan ikirari na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Iran ta sanar da lalata wani jirgin leƙen asirin Amurka samfurin E-3 Sentry a sansanin sojin sama na Prince Sultan dake kusa da birnin Riyadh.

Harin, wanda aka kai ranar 27 ga Maris ta hanyar amfani da makaman linzami da jirage marasa matuƙi, ya yi sanadiyyar raunata sojojin Amurka aƙalla 12.

Hotunan da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna jirgin ya ƙone kurmus inda yake fake. Masana tsaro sun ce ko da bam bai bugi jirgin kai-tsaye ba, fashewar makami a kusa da shi na iya ƙone shi saboda yadda jirgin yake da saurin kama wuta.

Kara karanta wannan

Wuya ta yi wuya: Isra'ila ta dakatar da kai hare hare kan kasar Iran, an ji dalili

Asarar jiragen yaƙi da Amurka ta yi

Rahotanni daga kafar yaɗa labaran Time of India sun nuna cewa Amurka ta yi asarar jiragen yaƙi aƙalla 16 tun farkon wannan rikici da Iran.

Daga cikin waɗannan har da jiragen MQ-9 Reaper guda 10 da maƙiya suka harbo, yayin da wasu suka lalace a hare-haren makaman linzami da aka kai sansanonin soji daban-daban.

Babban rashi mafi muni ya faru ne ta hanyar hatsari, inda aka kakkabo jiragen yaƙin F-15 guda uku ta hanyar kuskure a ƙasar Kuwait.

Haka kuma, wani jirgin dakon mai samfurin KC-135 ya fashe a sararin samaniya yayin aikin zuba mai, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dukkan ma'aikata shida dake cikinsa.

Amurka ta rasa akalla manyan jiragen yaki 16 tun bayan fara yaki da Iran.
Jirgin yaki marar matuki na Amurka samfurin MQ-9 Reaper. Hoto: Miguel J. Rodriguez Carrillo / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Yanayin yaƙin sama da tasirinsa

Masu sharhi kan al'amuran soja sun bayyana cewa yawan zirga-zirgar jiragen yaƙin Amurka a wannan yaƙi ya fi na lokacin yaƙin tekun Fasha.

Wannan ya sa asarar jiragen ta yi yawa, musamman jiragen MQ-9 waɗanda aka tsara su domin yin ayyuka masu haɗari domin ba su da matuƙi a cikinsu.

Kara karanta wannan

Iran ta harbo jirgin yaƙin Amurka, an sanya ladar kudi ga wanda ya kamo matuƙan

A halin da ake ciki, Iran na ci gaba da ƙarfafa gwiwa ga dakarunta, yayin da Amurka ke fuskantar matsin lamba kan yadda take gudanar da ayyukanta a Gabas ta Tsakiya.

Iran ta harbo jirgin yakin Amurka

A wani labari, mun ruwaito cewa, sojin Amurka da ta Isra'ila sun tabbatar da cewa Iran ta harbo wani jirgin yaƙin Amurka a sararin samaniyarta a ranar Juma'a.

Rahoto ya nuna cewa Amurka ta tura dakarun ceto na musamman domin gano matuƙan jirgin kafin dakarun Iran su yi awon gaba da su.

A hannu daya, ita kuma Iran ta sanya lada mai tsoka ga duk wanda ya bada bayanin ko ya kamo wadannan matuka da suka fada kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com