An Kwantar da Trump a Asibiti bayan Kamuwa da Rashin Lafiya? An Samu Gaskiya
- Fadar White House na Amurka ta yi karin haske kan rade-radin cewa Donald Trump yana asibitin Walter Reed domin samun kulawa
- Jita-jitar ta biyo bayan sanarwar cewa shugaban ba zai fito bainar jama’a ba a ranar wanda ya tayar da maganganu a tsakanin mutane
- Trump ya kuma yi gargadi ga kasar Iran da ba ta wa’adin awa 48 kan yarjejeniya ko daukar matakin soja a yakin da ake yi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Fadar White House ta fitar da wata sanarwa mai ban mamaki kan rade-radin cewa Donald Trump ba shi da lafiya.
Fadar ta karyata rade-radin da ke yawo cewa shugaban Amurka, Donald Trump, yana asibitin Walter Reed.

Source: Getty Images
Sanarwar ta zo ne bayan wasu sakonni a kafafen sada zumunta suka bazu cikin gaggawa, suna ikirarin cewa an garzaya da Trump asibiti, cewar International Business Times.

Kara karanta wannan
An fara magana bayan shafe kwanaki babu ɗuriyar Trump, fadar White House ta magantu
An bayyana halin da Trump ke ciki
Daraktan hulda da jama’a na White House, Steven Cheung, ya bayyana cewa shugaban yana ci gaba da aiki a fadar gwamnati da ofishin Oval a lokacin hutun Easter.
Ya ce wadannan ikirari ba su da tushe, duk da cewa sun samu dubban masu kallo cikin kankanin lokaci a intanet.
Jita-jitar ta fara ne bayan White House ta sanar cewa shugaban ba zai yi wani bayyanar jama’a ba a sauran ranar, abin da ya jawo tambayoyi daga jama’a.
Duk da cewa irin wannan sanarwa abu ne na yau da kullum, lokaci da yanayin da aka fitar da ita ya sa wasu suka fara zargin akwai wani abu da ake boyewa.

Source: Getty Images
Jita-jitar da aka taba yadawa kan Trump
A baya ma, an taba danganta sunan Donald Trump da asibitin Walter Reed, musamman lokacin da ya kai ziyara ba tare da sanarwa ba a shekarar 2019.
Haka kuma, a shekarar 2025, ya kai ziyara sau biyu domin duba lafiyarsa, ciki har da yin gwajin MRI, wanda likitansa ya ce yana cikin koshin lafiya.
Sai dai an taba bayyana cewa yana fama da wata cuta mai suna 'chronic venous insufficiency', wadda ke shafar yadda jini ke dawowa zuciya daga kafafu.
A wani bangare daban, Trump ya yi gargadi ga Iran cewa tana da awa 48 kacal ta cimma yarjejeniya ko kuma ta bude mashigar Hormuz kafin Amurka ta dauki matakin soja.
Wannan gargadi na daga cikin jerin matakan da ke nuna yadda rikicin siyasar waje ke kara tsananta a wannan lokaci, cewar rahoton Times Now.
Iran ta fadi shirin da ta yi kan Amurka
Mun ba ku labarin cewa kasar Iran ta sake sauya salon yakinta da Isra'ila da Amurka a Gabas ta Tsakiya bayan tura sababbin na’urorin kariyar sama.
Hare-haren Amurka da Isra’ila sun kai hari wurare da dama ciki har da tashar nukiliya ta Bushehr wanda ke da matukar tasiri a kasar.
Rahotanni sun ce dubban mutane sun mutu ko jikkata yayin da rikicin ke kara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya da ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
Asali: Legit.ng
