An Fara Magana bayan Shafe Kwanaki Babu Ɗuriyar Trump, Fadar White House Ta Magantu
- Ana ci gaba da maganganu bayan rashin ganin Shugaban Amurka Donald Trump na wasu kwanaki yayin da ake ci gaba da yaki
- Majiyoyi suka ce Trump ya kauracewa fitowa bainar jama’a a Washington, D.C., yayin da fadar White House ta ce yana aiki ba dare ba rana
- Rashin bayyanarsa ya biyo bayan harbo jirgin yakin Amurka da Iran ta yi, inda aka ceto mutum daya, dayan kuma yana bace har yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar ce.
Washington DC, US - Ana ta ce-ce-ku-ce game da rashin fitowar Shugaban Amurka Donald Trump bainar jama’a ba tsawon kwanaki yayin da ake yaki tsakanin Iran da Isra'ila.
Majiyoyi sun ce yana ci gaba da zama a Washington, D.C. yayin da jami’an White House ke cewa yana aiki tukuru domin ganin ya inganta Amurka.

Source: Getty Images
Rahoton Forbes ya tabbatar da cewa Trump bai bayyana ba tun ranar Laraba 1 ga watan Afrilun 2026 da ta wuce.
Yadda Iran ta harbo jirgin Amurka
Rahotanni sun ce Iran ta harbo jirgin yakin Amurka nau’in F-15E, inda aka ceto daya daga cikin ma’aikatan jirgin, yayin da dayan kuma yake bacewa har yanzu.
Kasashen Amurka da Iran sun fara bincike domin gano matukin jirgin da ya bace, yayin da kafafen Iran ke kira ga jama’a su taimaka da lada.
Trump bai yi karin bayani ba kan lamarin, sai dai ya ce hakan ba zai hana ci gaba da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran ba.
Shugaban ya bai wa Iran wa’adin awanni 48 ta bude Strait of Hormuz ko kuma ta cimma yarjejeniya kafin wa’adin da ya gindaya ya kare.
Ya gargadi Iran cewa idan ba ta bi wannan sharadi ba, to Amurka za ta dauki mataki mai tsauri, yana mai cewa “duk wani bala’i zai sauka”.

Kara karanta wannan
Rashin taya Trump yaki da Iran ya harzuƙa shi, ya ci mutuncin Shugaban Faransa da matarsa

Source: Getty Images
Jita-jitar da ake yadawa kan Donald Trump
An ce bayyanarsa ta karshe ita ce lokacin da ya ziyarci kotun koli tare da gabatar da jawabi kan rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran, cewar International Business Times.
Wasu majiyoyi sun fara yada cewa wai rashin bayyanar shugaban na da alaka da zargin rashin lafiya da aka ce yana asibiti.
Duk da cewa ba a tabbatar da labarin ba, wasu sun ce an kai shugaban asibitin Walter Reed domin ba shi kulawa ta musamman.
Yakin Iran: Trump ya nemi a tsagaita wuta
A baya, an ji cewa majiyoyi sun nuna kasar Amurka karkashin shugaba Donald Trump ta nemi a tsagaita wuta a yakin da aka fara a karshen watan Fabrairun 2026.
Hakan na zuwa ne bayan shafe kwanaki ana gwabza fadan da ya jawo mutuwar mutane da dama da lalata kadarorin biliyoyin daloli a duniya.
Shugaba Donald Trump ya yi bayani game da harbo jirgin Amurka da dakarun Iran suka yi da makomar sulhun da ya ce an fara maganar tun a kwanakin baya.
Asali: Legit.ng
