Kasashen Afirka 3 da Kasar Isra’ila Ta Taɓa Kai Masu Farmaki a Baya

Kasashen Afirka 3 da Kasar Isra’ila Ta Taɓa Kai Masu Farmaki a Baya

  • Yakin Iran da Isra’ila na ci gaba da tayar da hankali a duniya duba da asarar rayuka da dukiyoyin al'umma da ake yi
  • Isra'ila ta taba kai hare-hare a wasu kasashen Afirka a tarihi, lamarin da ya shafi siyasa da tsaron yankin
  • A wasu kasashen, an kai hare-haren sama kan masana’antu da ayarin makamai, yayin da a wasu aka gudanar da harin domin ceto fasinjoji

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Ana ci gaba da yaki tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka karkashin jagorancin Donald Trump.

Rahotanni sun nuna cewa Isra’ila ba ta takaita ayyukan sojinta a Gabas ta Tsakiya kadai ba, domin ta taba kai hare-hare a wasu sassan Afirka.

Kasashen Afirka da Isra'ila ta kai wa hari
Wani yanki a kasar Sudan da Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Donwilson Odhiambo.
Source: Getty Images

Kasashen Afirka da Isra'ila ta kai hari

Kara karanta wannan

Bana ka taba: Faransa ta tura sojoji da tankokin yaki domin a yaki Isra'ila

Wadannan hare-hare sun hada da farmaki a Sudan, harin Entebbe a Uganda, da kuma mamayar Masar a lokacin rikicin Suez, cewar Binciken Al Jazeera Centre for Studies.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa hare-haren sun yi tasiri mai girma a siyasar yankuna da duniya baki daya.

Legit Hausa ta yi duba kan kasashe da Isra'ila ta taba kai masu hari a yankin Nahiyar Afirka.

1. Sudan: Hare-haren sama da ayyukan sirri

A watan Oktoba na shekarar 2012, NPR ta ruwaito cewa wani jami’in leƙen asirin Isra’ila ya tabbatar da cewa an gudanar da ayyukan soji a Sudan.

Wannan ya biyo bayan zargin da gwamnatin Sudan karkashin Omar Al-Bashir ta yi cewa Isra’ila ta kai hari kan wata masana’antar makamai da ke wajen Khartoum.

Isra’ila ta tura jiragen yaki guda hudu domin kai hari kan wata masana’antar makamai da ke gefen Khartoum da asuba, inda aka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu da dama.

Wannan ba shi ne karo na farko ba, a shekarar 2009, an lalata wani ayarin makamai a gabashin Sudan ta hanyar harin sama, cewar rahoton BBC.

Kara karanta wannan

Kwan gaba kwan bayan Donald Trump a yakin Amurka da Iran

A shekarar 2011 kuma, wani harin makami mai linzami kusa da Port Sudan ya kashe mutane biyu, daya daga cikinsu babban mai sayen makamai ne ga Hamas.

Wadannan hare-hare da aka maimaita sun nuna yadda Isra’ila ke kokarin dakile hanyoyin safarar makamai ta Sudan.

Musabbabin harin Isra'ila a Sudan
Tsohon shugaban kasar Sudan, Omar Al-Bashir. Hoto: ASHRAF SHAZLY.
Source: Getty Images

2. Uganda: Harin Entebbe

Harin Isra’ila a Entebbe, wanda aka fi sani da 'Operation Entebbe', ya faru a watan Yuli na shekarar 1976.

Bayan an sace jirgin saman Air France da ‘yan ta’adda hudu (Palasdinawa biyu da Jamusawa biyu), an karkatar da jirgin zuwa Entebbe a Uganda, inda Shugaban kasar mai mulkin kama-karya, Idi Amin, ya tarbi ‘yan ta’addan.

‘Yan ta’addan sun bukaci a sako fursunoni da ake tsare da su a Isra’ila da Turai, kamar yadda Daily Monitor ta ruwaito.

A ranar 4 ga Yuli, sojojin Isra’ila na musamman sun kaddamar da wani harin ceto mai hatsari a filin jirgin saman Entebbe.

Sun kubutar da mutane 102 da aka yi garkuwa da su, sun kashe ‘yan ta’adda uku, sannan mutane biyu daga cikin wadanda aka sace sun mutu a yayin musayar wuta.

Kara karanta wannan

Amurka ta ci karo da cikas, Iran ta illata ta a yakinta da kasar Isra'ila

Wannan aiki ya zama abin koyi a tarihin yaki da ta’addanci, inda ya kara wa Isra’ila karfin gwiwa a kasa, tare da matukar raunana martabar Idi Amin a idon duniya.

Yadda Isra'ila ta kai hari a Uganda
Tsohon shugaban kasar Uganda lokacin da Isra'ila ta kai hari, Idi Amin. Hoto: Bettmann.
Source: Getty Images

3. Masar: Harin rikicin Suez

A ranar 29 ga Oktoba, 1956, Isra’ila ta kai hari kan Masar a lokacin rikicin Suez, rundunonin Isra’ila guda 10 sun kutsa zuwa mashigin ruwan Suez, inda suka fatattaki sojojin Masar.

Biritaniya da Faransa sun shiga rikicin nan da nan, inda suka bukaci a janye sojoji tare da kaddamar da nasu harin soja.

A ranakun 5 da 6 ga Nuwamba, sojojin kasashen biyu sun kwace iko da Port Said da Port Fuad, History.com ta ruwaito labarin.

Sai dai matsin lamba daga manyan duniya, musamman Amurka da kuma Majalisar Dinkin Duniya, ya tilasta tsagaita wuta, daga bisani, sojojin Isra’ila sun janye a watan Maris na shekarar 1957.

Wannan lamari ya zama daya daga cikin manyan hare-haren farko da Isra’ila ta yi a nahiyar Afirka, wanda ke da alaka da fafatawar siyasa da iko kan mashigin ruwan Suez.

Isra'ila ta kai hari a Masar tun a shekarar 1956
Firayim ministan Isra'ila na yanzu, Benjamin Netanyahu. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Yakin Iran/Isra'ila na barazana ga kasashen Afirka

Kara karanta wannan

Isra'ila ta bar boye boye, ta bayyana adadin waɗanda suka jikkata a yaki da Iran

A wani labarin, kun ji cewa hukumar kula da abinci ta duniya ta yi gargadin cewa mutane miliyan 10.4 a Yammaci da Tsakiyar Afirka na iya fuskantar yunwa.

Rikicin Iran da isra’ila tare da Amurka na iya haddasa matsalar abinci a duniya wanda har yanzu ake ci gaba da yi.

Har ila yau, kungiyar inganta noma da abinci ta ce kasashe 31 a Afirka na bukatar tallafin abinci ciki har da Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.