An tura tsohon shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir gidan kurkuku
- Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa an tisa keyar tsohon shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir zuwa gidan yari
- Yanzu haka dai sojojin kasar sun tabbatar da cewa yana nan an killace shi a wani gidan yari dauke da matakan tsaro
An tura tsohon shugaban kasar Sudan, Omar Al-Bashir, gidan kurkukun Khartoum, bayan sojojin kasar sun hambarar da shi daga kujerar shi a makon da ya gabata, wata majiya mai karfi ta sanar da hakan a yau Larabar nan.
"An tura Omar Al-Bashir gidan kurkukun Kober da ke birnin Khartoum," wani mutumi ne ya bayyana haka, inda ya nemi a boye sunan shi saboda tsaro.
Sojojin kasar Sudan sun hambarar da gwamnatin shugaba Omar Al-Bashir ranar Alhamis din da ta gabata, bayan 'yan kasar sun kwashe watanni hudu suna zanga zanga akan irin mulkin mallakar da ya ke yi a kasar. Shugabannin sojin kasar sun bayyana cewa yanzu haka yana nan a tsare a hannunsu.
KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin rataye wasu mutane guda 7
Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa akwai zirga zirgar jami'an hukumomin tsaro a gidan kurkukun Kober da ke birnin Khartoum.
"Akwai sojoji a manyan motoci dauke da manyan bindigogi masu linzami a kofar gidan kurkukun Kober," in ji majiyar.
A satin da ya gabata ne shugabannin sojojin kasar Sudan karkashin jagorancin ministan tsaron kasar suka hambarar da gwamnatin shugaban kasar Omar Al-Bashir, bayan shafe watanni ana gabatar da zanga zanga a fadin kasar.
Shugabannin sojojin sun bayyana cewa sai nan da shekaru biyu za su bayar da mulkin ga farar hula domin cigaba da gabatar da mulkin demokuradiyya a kasar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng