Ran Rasha Ya Baci kan Harin Isra'ila a Tashar Nukiliyar Iran, Ta Fadi Abin da Take Yi

Ran Rasha Ya Baci kan Harin Isra'ila a Tashar Nukiliyar Iran, Ta Fadi Abin da Take Yi

  • Kasar Rasha ta yi martani mai zafi kan harin makami mai linzami da aka kai kusa da tashar nukiliyar Bushehr a Iran
  • Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova, ta ce harin laifi ne, tana mai nuna damuwa kan ƙarin tashin hankali
  • Hukumar nukiliyar duniya ta IAEA ta gargadi cewa kai hari kan tashoshin nukiliya da wuraren da ke kusa da su ba abin yarda ba ne

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Moscow, Russia - Kasar Rasha ta yi kakkausar suka kan sabon harin makami mai linzami a Iran a yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

Rasha na magana ne da aka kai hari kusa da tashar nukiliyar Bushehr, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum guda.

Rasha ta nuna bacin ranta kan harin Isra'ila a Iran
Shugaba Masoud Pezeshkian da Vladimir Putin na kasar Rasha. Hoto: Vladimir Putin.
Source: Facebook

Rasha ta fusata bayan hari a Iran

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta kara azama a yaki da Isra'ila, ta fadi shirinta kan jiragen Amurka

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova, ta ce suna karɓar rahotanni cikin damuwa kan harin da ya faru ranar 4 ga Afrilun 2026, cewar Al Jazeera.

Ta ce gwamnatin Rasha na nazarin bayanan da ke shigowa, tare da bayyana harin a matsayin laifi mai muni da ya janyo asarar rayuka.

Zakharova ta kuma mika ta’aziyya ga iyalan wanda ya mutu, wanda aka ce yana kula da tsaron tashar nukiliyar Bushehr.

Tun da fari, shugaban kamfanin Rosatom, Alexey Likhachev, ya ce al’ummar duniya sun nuna damuwa sosai kan harin da aka kai kusa da tashar.

Ya bayyana cewa shugaban Hukumar IAEA ya yi magana, tare da cewa hulɗa da ƙasashe abokan hulɗa ta nuna ƙaruwa damuwa kan rikicin.

Likhachev ya ƙara da cewa kowa na cikin fargaba kan yadda rikicin ke ƙara tsananta, lamarin da ke iya janyo matsala mai girma a duniya.

Rasha ta fusata game da hari a Iran
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin Hoto: Vladimir Putin.
Source: Getty Images

Martanin Hukumar kula da makamashin nukiliya

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran ta tabbatar da cewa an sake kai wani hari kusa da tashar nukiliyar Bushehr ranar Asabar.

Ta ce wani abu mai fashewa ya faɗi kusa da tashar, inda ya kashe jami’in tsaro guda, amma bai lalata manyan kayayyakin tashar ba.

Kara karanta wannan

Iran ta lissafo wuraren da za ta kai wa hari idan Amurka ba ta shiga taitayinta ba

Hukumar IAEA ta jaddada cewa kai hari kan tashoshin nukiliya ko wuraren da ke kusa da su ba abin yarda ba ne saboda haɗarin tsaro.

Rasha ta fara kwashe ma’aikata 198 daga tashar nukiliyar Bushehr ta Iran bayan wani makami mai linzami ya fadi kusa da wurin, cewar Turkiye Today.

Jami’an Iran da kafafen yada labarai sun ce an kai hare-hare sau da dama a wurin, tare da gargadin cewa hakan na iya jefa Iran da yankin Gulf baki daya cikin hadari.

Wannan ba shi ne karon farko ba da ake kai hari kusa da tashar, ko ranar 17 ga watan Maris, 2026 ma an kai wani hari a ma'aikatar amma babu barna da aka samu.

Iran ta yi wa Amurka, Isra'ila gargadi

A baya, mun kawo rahoto cewa dakarun 'Islamic Revolutionary Guard Corps' a Iran watau IRGC ta yi gagarumar barazana ga Amurka da Isra'ila a yakin da ake yi.

IRGC ta yi barazanar kai hari kan jami’o’in Amurka a Gabas ta Tsakiya bayan hare-haren da suka lalata wasu jami’o’i a Iran.

Ta bukaci Amurka ta yi Allah-wadai da harin kafin wa’adin da aka sanya, tare da gargadin ma’aikata da dalibai su guji kusantar harabar jami’o’i.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.