Amurka Ta Ba wa Iran Wa'adin Awanni a Sabuwar Barazana kan Mashigar Hormuz
- Shugaban Amurka, Donald J Trump ya bai wa Iran wa’adin awa 48 ta bude hanyar wucewar jiragen ruwa ta Hormuz
- Donald Trump ya yi gargadin cewa lokaci na kurewa Iran daga wa'adin da aka ba ta na bude mashƙƙuigar Hormuz a cikin gaggawa
- Kalaman sun kara tayar da hankali kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya musamman bayan hare-hare kan wuraren makaman Iran
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Iran – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake jaddada matsayinsa kan Iran, inda ya bukaci kasar ta bude mashigar ruwa ta Hormuz cikin gaggawa.
Donald Trump ya bayyana cewa a wannan karon, ya ba wa Iran wa'adin awanni 48 na bude Hormuz idan tana son kanta da lafiya.

Source: Twitter
Trump ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, inda ya ce lokaci na kurewa ga Iran ta dauki mataki kafin a dauki wani tsauraran mataki a kanta.
Amurka ta sake yi wa Iran barazana
A cikin sakon nasa, Donald J Trump ya yi wai waye a kan wani gargadi da ya taba yi wa Iran a baya na ta gaggauta bude mashigar.
Donald Trump ya bayyana cewa:
“Kun tuna lokacin da na bai wa Iran kwanaki goma ta kulla yarjejeniya ko ta bude mashigin hormuz?”
Ya kara da cewa:
“Lokaci na kurewa – saura awa 48 kafin duk wata mummunar illa ta sauka a kansu.”
Trump na ci gaba da matsin lamba kan Iran, musamman kan batun mashigar Hormuz wanda ke da matukar muhimmanci ga harkokin sufuri da tattalin arzikin duniya.
Gargadin Trump ya kara dagula yanayin tsaro
Masu lura da al’amuran siyasa na kasa da kasa na ganin cewa wannan sabon gargadi daga Trump na iya kara dagula yanayin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.
Mashigar Hormuz na daya daga cikin muhimman hanyoyin ruwa a duniya da ake bi wajen jigilar danyen mai, kuma duk wata matsala a yankin na iya haifar da tashin farashin mai da kuma rikicewar kasuwannin duniya.
Ko da yake Trump bai fayyace irin matakin da za a dauka ba idan Iran ba ta bi umarnin ba, kalamansa na nuni da yiwuwar daukar matakin soja ko karin takunkumi.

Source: Getty Images
Har yanzu Iran ba ta mayar da martani kai tsaye kan wannan sabon gargadi ba. Sai dai masana na ganin cewa irin wadannan kalamai kan kara tsananta alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
A halin yanzu, hankula sun karkata kan yadda Iran za ta dauki wannan wa’adi, da kuma yiwuwar tasirin hakan ga zaman lafiya da tsaron yankin baki daya.
Iran ta ƙara zama a yaƙin Amurka
A wani labarin, kun ji cewa ƙasar Iran ta sake sauya salon yakinta da Isra'ila da Amurka a Gabas ta Tsakiya bayan tura sababbin na’urorin kariyar sama.
Hare-haren Amurka da Isra’ila sun kai hari wurare da dama ciki har da tashar nukiliya ta Bushehr da ke kasar, lamarin da ya ke ƙara daga hankalin duniya.
Rahotanni sun ce dubunnan mutane sun mutu ko jikkata yayin da rikicin ke kara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya a yaƙin da aka fara a ƙarshen Fabrairu, 2026.
Asali: Legit.ng


