Kasar Iran Ta Kara Azama a Yaki da Isra’ila, Ta Fadi Shirinta kan Jiragen Amurka

Kasar Iran Ta Kara Azama a Yaki da Isra’ila, Ta Fadi Shirinta kan Jiragen Amurka

  • Kasar Iran ta sake sauya salon yakinta da Isra'ila da Amurka a Gabas ta Tsakiya bayan tura sababbin na’urorin kariyar sama
  • Hare-haren Amurka da Isra’ila sun kai hari wurare da dama ciki har da tashar nukiliya ta Bushehr da ke kasar
  • Rahotanni sun ce dubban mutane sun mutu ko jikkata yayin da rikicin ke kara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Rahotanni sun bayyana cewa kasar Iran ta tura sababbin tsarin kariya a sama domin kare sararin samaniyarta.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa hakan na da nasaba da shirin tinkarar jiragen yakin Amurka yayin da yakin ke kara tsananta.

Iran ta sake tura na'urorin domin illata jiragen Amurka
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei, Shugaba Donald Trump na Amurka da Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump, Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Shirin yakin da Iran ta yi wa Amurka

Hukumomin sojin kasar sun ce tsarin ya taimaka wajen harbo wasu jiragen yaki, tare da alkawarin cewa za su tabbatar da cikakken iko a sararin samaniyarsu, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Bana ka taba: Faransa ta tura sojoji da tankokin yaki domin a yaki Isra'ila

A gefe guda kuma, rahotanni sun nuna cewa hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra’ila sun kai tashar nukiliya ta Bushehr, inda aka tabbatar da mutuwar mutum guda.

Sai dai ba a tabbatar da ko harin ya haifar da zubar lalata injin nukiliyar ba, yayin da ake ci gaba da tattara bayanai kan barnar.

Rahotanni sun kuma ce an harbo wani jirgin yaki na Amurka a sararin Iran, lamarin da ke nuna karuwar arangama kai tsaye tsakanin bangarorin biyu, cewar TRT World.

Iran ta harbo jirgin yakin Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka a birnin New York. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Iran ta harba makamai kasashe makwabta

Wani jami’in Amurka ya tabbatar da harbo jirgin kasar, yayin da ake kokarin ceto matukan jirgin a yankin tsakiyar kasar Iran.

Haka kuma, rahotanni sun ce Iran ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuki da dama kan wasu kasashe makwabta, ciki har da Jordan.

Sai dai dakarun Jordan sun ce sun dakile yawancin hare-haren, duk da cewa wasu sun kai ga wuraren da aka nufa.

Bugu da kari, rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun shafi cibiyoyin ilimi da masana’antu a Iran, inda sama da jami’o’i 30 suka gamu da hari tun farkon rikicin.

Kara karanta wannan

Amurka ta ji wuta, Trump ya nemi a tsagaita wuta a yakin da ake yi da Iran

Adadin mutanen da suka mutu da jikkata ya karu sosai, inda rahotanni ke nuna cewa dubban mutane sun rasa rayukansu yayin da daruruwan dubban suka rasa matsugunansu.

A halin yanzu, kasashe da dama na kira da a dakatar da rikicin tare da komawa kan tattaunawa domin kauce wa karin tabarbarewar lamura.

Iran/Isra'ila: Najeriya da kasashe 39 sun yi zama

A wani labarin, an ji cewa ana tsaka da yaki, kasashe 40 ciki har da Najeriya sun gudanar da taro domin nemo hanyoyin dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin Hormuz.

Hakan ya biyo bayan matakin rufe mashigar da Iran ta yi dalilin yakin da ake yi tsakanin ta da Isra'ila da Amurka a Gabas ta Tsakiya.

Barazanar hare-haren Iran da ramuwar gayya ta dakatar da zirga-zirga a mashigar, lamarin da ya jawo tashin farashin mai a duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.