Hare Haren Iran Sun Yi Barna a Isra'ila, Mutane da Dama Sun Jikkata
- Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai hare-hareta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan Isra'ila yayin da ake ci gaba da gwabza fada
- Ma'aikatar lafiya ta Isra'ila ta bayyana cewa mutane da dama sun samu raunuka sakamakon hare-haren a cikin sa'o'i 24 da suka gabata
- Hakazalika ma'aikatar ta bayyana cewa adadin mutanen da suka samu raunuka tun bayan fara yaki da Iran ya haura 6,500
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv, Isra'ila - Ma’aikatar lafiya ta Isra'ila ta bayyana adadin mutanen da suka jikkata a cikin sa'o'i 24.
Ma'aikatar lafiyan ta bayar da rahoton cewa, a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an kai mutane 148 da suka ji rauni zuwa asibitoci sakamakon rikicin da ake yi da Iran.

Source: Twitter
Jaridar The Times of Israel ta kawo rahoton mutanen da suka jikkata a ranar Juma'a, 3 ga watan Afirilun 2026.
Mutanen da suka jikkata a Isra'ila
Lamarin dai ya sa adadin mutanen da aka kwantar a asibiti tun farkon faɗan ya haura 6,500, tashar Aljazeera ta kawo labarin.
Daga cikin waɗanda aka yi wa magani a asibitoci a ranar da ta gabata, mutane huɗu na cikin wani hali na matsakaici, yayin da mutane 108 ke cikin kyakkyawan yanayi.
Mutane biyar ne ake ci gaba da duba lafiyarsu, yayin da aka yi wa mutane 31 maganin firgici da fargaba sakamakon tashin hankalin.
Ma’aikatar ta ce tun farkon fara yaƙin da Iran a ranar 28 ga Fabrairu, an kwantar da mutane 6,594 a asibitoci, inda a halin yanzu mutane 124 ke ci gaba da jinya a asibitin.
Ma’aikatar ba ta bayar da dalla-dalla kan abubuwan da suka janyo raunin kowane mutum ba.
Ana ci gaba da yaki tsakanin Iran, Isra'ila
Wasu raunukan ka iya kasancewa mutane ne suka ji su yayin ƙoƙarin guduwa zuwa wuraren boyewa, ba wai lallai kai-tsaye daga harin makamai masu linzami daga Iran ko na roka daga Lebanon ba.

Source: Getty Images
Wannan adadi na waɗanda suka jikkata ya haɗa da sojoji da kuma farar hula baki ɗaya.
Isra'ila Amurka dai sun kaddamar da hare-hare ta sama kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026.
Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan Isra'ila da sansanonin sojojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban Iran ya aika wasika ga Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Amurka yayin da ake ci gaba da yaki.
Shugaba Pezeshkian ya yi fatali da yadda ake nuna Iran a matsayin barazana ga tsaro, yana mai cewa hakan ba daidai ba ne.
Masoud Pezeshkian ya ya jaddada cewa a tarihin Iran na tsawon zamani, ba ta taɓa zaɓar hanyar ta’addanci, mamaya, mulkin mallaka, ko danniya ba.
Asali: Legit.ng

