Iran Ta Zafafa Hare Hare kan Isra'ila, Miliyoyin Yahudawa Sun Shiga Matsala

Iran Ta Zafafa Hare Hare kan Isra'ila, Miliyoyin Yahudawa Sun Shiga Matsala

  • Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta farmaki biranen Tel-Aviv da Haifa na Isra'ila
  • IRGC ta kai farmakin ne a rukuni na 91 na hare-haren ramuwar gayya da take kai wa wanda ta yi lakabi da suna 'Operation True Promise 4'
  • Rundunar ta bayyana cewa hare-haren sun yi barna tare da sanya miliyoyin mutane neman mafaka a mabuya

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) ta sanar da kaddamar da harin makamai masu linzami kan Isra'ila.

IRGC ta kaddamar da harin ne a matsayin rukuni na 91 na jerin ayyukanta na Operation True Promise 4, inda ta farmaki tsakiyar biranen Tel Aviv da Haifa na Isra'ila.

Iran ta kai hare-hare kan Isra'ila
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: @drpezeshkian, @netanyahu
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da IRGC ta fitar a daren Alhamis, 2 ga watan Afirilun 2026, kamar yadda tashar Press tv ta Iran ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Ba sauki: Amurka da Isra'ila sun ga ta kansu, Iran ta kaddamar da zazzafan hari

Mutanen Isra'ila sun shiga maboya

IRGC ta bayyana cewa hare-haren sun tilasta wa mazauna Isra'ila kusan miliyan 5 neman mafaka a cikin ramin buya na karkashin kasa.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa dakarun Yemen sun fara kaddamar da nasu hare-haren zuwa Kudancin yankunan da Isra'ila ta mamaye da kuma yankin Dimona.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Karar fashe-fashe akai-akai ta jefa ma'aikatan agajin gaggawa cikin rudani da fafutukar shawo kan lamarin."

An yi wa Isra'ila taron dangi

Tashar Aljazeera ta ce wani kakakin soja na kungiyar Ansarullah ta Yemen ya sanar da cewa, tare da hadin gwiwar Iran da kungiyar Hezbollah, an gudanar da wani harin hadin gwiwa na musamman kan muhimman wuraren makiya a yankin Jaffa na Tel Aviv.

Kakakin ya jaddada cewa harin ya nuna yadda dakarun bangarorin uku suka hada kai wajen gudanar da ayyukansu na adawa a yankin.

A cikin 'yan sa'o'in da suka gabata, IRGC ta kaddamar da jerin hare-hare ta hanyar amfani da manyan makamai masu linzami da jirage marasa matuka, inda ta farmaki sansanonin dakarun Isra'ila da na Amurka.

Kara karanta wannan

Yaki ya rincabe: Iran ta harba makamai 300 lokaci 1 kan sojojin Amurka da Isra'ila

Iran ta farmaki muhimman wurare a Isra'ila

Rahotanni sun nuna cewa sansanonin sojojin saman Isra'ila masu muhimmanci, ciki har da Tel Nof, Palmachim, da filin jirgin sama na Ben Gurion, sun fuskanci munanan hare-hare.

Iran ta kai hari kan Isra'ila
Makami mai linzami na Iran da aka harba Hoto: @IRIran_Military
Source: Twitter

Bugu da kari, wuraren taron sojoji a biranen Tel Aviv, Haifa, Eilat, yankin Negev, da Beersheba su ma sun fuskanci ruwan makamai masu linzami da na jirage marasa matuka wanda ya janyo barna mai yawa da asarar rayuka.

A gefe guda kuma, sansanonin sojojin Amurka da ke yankin ba su tsira ba. Sansanonin Amurka da ke Ahmed al-Jaber da Ali al-Salem a Kuwait, da kuma sansanin al-Kharj da ke Saudiyya, duk sun fuskanci harin kwararrun makamai masu linzami, inda suka tafka gagarumar barna.

Iran ta farmaki sansanin sojojin Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin kasar Iran ta farmaki sansanin sojojin saman Amurka da ke Jordan.

Rundunar sojojin ta Iran ta kai harin ne kan jiragen yakin da ke jibge a wani sansanin sojojin Amurka a ƙasar Jordan.

A cewar rundunar sojojin, an kai harin ne da nufin raunana ƙarfin abokin gaba na yin yaƙi ta sama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng