Barazanar da Trump Ya Sake Yi wa Kasar Iran, Ya Fadi Barnar da Ya Yi Mata a Yaki
- Shugaba Donald Trump na Amurka ya sake magana kan yaki da Iran tare da yin barazana game da kai hare-hare
- Trump ya ce Amurka ce ta lalata babbar gada mafi girma a Iran, yana gargadin cewa akwai karin hare-hare nan gaba
- Rahotanni sun ce mutane takwas sun mutu, 95 sun jikkata bayan harin da ya raba gadar biyu, daya daga manyan ayyukan more rayuwa a Iran
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump ya dauki alhakin lalata babbar gada mafi girma a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Hakan ya biyo bayan Trump ya yi gargadin cewa zai kara kai hare-hare idan ba a cimma yarjejeniya ba.

Source: Twitter
Trump ya wallafa bidiyo da Al Jazeera ta samu da ke nuna yadda gadar B1 mai tsayin mita 136 ta ruguje tsakanin Tehran da Karaj.

Kara karanta wannan
Rashin taya Trump yaki da Iran ya harzuƙa shi, ya ci mutuncin Shugaban Faransa da matarsa
Harin da Amurka ta kai a Iran
Rahotannin kafafen yada labaran Iran sun ce akalla mutane takwas sun mutu yayin da wasu 95 suka jikkata, bayan an kai harin sau biyu a tsakiyar gadar.
Hotuna daga baya sun nuna gibin da ya bayyana a tsakiyar gadar, wacce ake kallon ta a matsayin daya daga manyan ayyukan gine-gine a kasar Iran.
Trump ya ce gadar ba za ta sake amfani ba, yana gargadin cewa “akwai karin abubuwa da za su biyo baya” idan har ba a samu sulhu ba.
Ba a tabbatar ko fararen hula na amfani da gadar lokacin harin ba, duk da cewa an ga wata mota a gefen gadar kafin ta ruguje.

Source: Getty Images
Trump ya sha alwashin kai hare-hare a Iran
A wani jawabi da ya gabatar, Trump ya ce yakin da Amurka da Isra’ila suka fara a ranar 28 ga Fabrairun 2026 yana dab da kammala tare da cimma manufofi.
Sai dai ya sake yin barazanar lalata dukkan tashoshin samar da wutar lantarki a Iran, wanda zai iya jefa miliyoyin mutane cikin duhu da wahala.
An kuma tabbatar da wasu hare-hare a Iran ciki har da wanda aka kai wani sansanin makamai masu linzami a Isfahan, inda aka ga gobara da fashe-fashe masu karfi.
Ana zargin Iran ta boye wasu kayan sinadarin 'uranium' masu karfi a Isfahan, wadanda za a iya amfani da su wajen kera makaman nukiliya idan aka kara inganta su.
Akwai rade-radin cewa Amurka na tunanin kai wani hari domin kwace wadannan kayan, duk da cewa Trump ya ce ba shi damu da su sosai ba, cewar The Guardian.
Iran ta bayyana cewa za ta dauki matakin ramuwar gayya mai tsauri, tana mai cewa yakin zai ci gaba har sai makiyanta sun mika wuya gaba daya.
Sharudan da Trump ya gindaya wa Iran
A wani labarin, an ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana game da yunkurin tsagaita wuta da Iran ta nema a yi a yaƙin da ake yi Trump ya ce.
Shugaban Iran yana neman tsagaita wuta, duk da sabanin kalamansa kan dakatar da yakin ko kara tsananta shi.
Iran ta ci gaba da kai hare-hare a yankin Tekun Fasha, yayin da farashin mai ya tashi sakamakon rikicin da ya shafi mashigar Hormuz.
Asali: Legit.ng
